‘Yan Sanda sun yi bayanin abin da ya sa su ke neman Shugaban Majalisar Dattawa

‘Yan Sanda sun yi bayanin abin da ya sa su ke neman Shugaban Majalisar Dattawa

Jiya kun ji labari cewa Jami'an 'Yan Sandan Najeriya sun gayyaci Shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki ya hallara a gaban su kan wani fashi da aka yi kwanaki a Jihar Kwara domin ya wanke kan sa.

‘Yan Sanda sun yi bayanin abin da ya sa su ke neman Shugaban Majalisar Dattawa

Shugaban Majalisar Dattawa ya fada hannun 'Yan Sanda

Mutane 22 da ake zargi da laifin fashi da makami a Garin na Offa sun shiga hannun ‘Yan Sanda. Daga ciki dai akwai mutum 5 da su ka ambaci sunan Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki.

Ga sunayen wadanda ake tunani su ka yi wannan danyen aiki nan:

1. Ayoade Akinnibosun

2. Ibukunle Ogunleye

3. Adeola Abraham

4. Salawudeen Azeez

5. Niyi Ogundiran

6. Michael Adikwu

7. Kabiru Afolabi

8. Omoseni Kassim

9. Kayode Opadokun

10. Kazeem Abdulrasheed

KUKARANTA: An kama wasu masu garkuwa da mutane a Osun

11. Azeez Abdullahi

12. Adewale Popoola

13. Adetoyese Muftau

14. Alexander

15. Richard Buba Terry

16. Peter Jasper Kuunfa

17. Ikechukwu Ebuka Nnaji

18. Moses Godwin

19. Adeola omiyale

20. Femi Idowu

21. Alabi Olalekan

22. Yusuf Abdulwahab

Daga cikin makaman da aka samu wajen su akwai:

1. Kanana bindiga ‘Yar hannu 2

2. Katuwar bindiga 1

3. Wata bindiga mai lugude 1

Akwai kuma motoci da su ka hada da:

1. Lexus Rx 300

2. Marsandi kirar Compressor

3. Toyota Prado da kuma

4. Toyota Camry

Daga cikin motocin akwai motar wani mai ba Gwamnatin Jihar Kwara shawara kan harkar siyasa. An kuma samu wata mota mai dauke da sunan Bukola Saraki a jikin ta.

Bayan nan kuma dai an samu:

1. Makudan kudi har N600, 000 da

2. Wayoyin salula 4

Daga cikin wadanda aka kama akwai mutane 5 da su ka tabbatar da cewa Shugaban Majalisar Dattawa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kwara watau Bukola Saraki shi ne Mai gidan su. Wadannan mutane su ne: Ayoade Akinnibosun, Ibukunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salawudeen Azeez, da kuma Niyi Ogundiran.

Wadannan mutane dai ba yau ake zargin su ka fara fashi ba kuma an yi nasarar kama su ne bayan an samu hoton wasu daga cikin su. Haka nan Alabi Olalekan wanda motar sa ta shiga hannun ‘Yan fashin yanzu yana hannun ‘Yan Sanda. Olalekan yana cikin masu ba Gwamnan Jihar Kwara shawara kan lamarin siyasa.

Yusuf Abdulwahab wanda shi ne Shugaban Ma’ikatan gidan Gwamnati na Jihar Kwara shi ma yana hannun ‘Yan Sanda yanzu. Ana zargin sa da kokarin tunbuke sunan Saraki daga daya daga cikin motocin da aka samu wajen ‘Yan fashin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel