Shugaba Buhari na tsoron zaben 2019

Shugaba Buhari na tsoron zaben 2019

Babbar jam'iyyar adawa PDP ta bayyana cewar fitowa takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari babbar matsala ce a gareshi, tunda a yanzu haka jam'iyyar APC bata da karfin da take dashi a zaben da ta lashe na 2015

Shugaba Buhari na tsoron zaben 2019

Shugaba Buhari na tsoron zaben 2019

Babbar jam'iyyar adawa PDP ta bayyana cewar fitowa takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari babbar matsala ce a gareshi, tunda a yanzu haka jam'iyyar APC bata da karfin da take dashi a zaben da ta lashe na 2015.

DUBA WANNAN: Sunayen ‘yan ta’addan da ‘yan sanda ke zargin Bukola Saraki da daukan nauyin aiyukan su

A bayanin da jam'iyyar tayi a jiya wanda ya fito daga bakin Sakataren jam'iyyar na kasa a fannin yada labarai, Kola Ologbondiyan, yace tsoron da shugabannin jam'iyyar APC suke ciki da kuma shugaba Buhari, ya samo asali saboda sun kasa cikawa 'yan Najeriya alkawarurrukan da suka dauka a lokacin kamfen din zaben daya gabata.

"Abin takaici ne irin abubuwan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yiwa jam'iyyar PDP na cewa ita azzalumar jam'iyya ce, amma kuma har yanzu yaki nuna 'yan Najeriya cewa ya kasa cika musu alkawarurrukan daya dauka a 2015.

"Sai dai kuma wani abu da shugaba Buhari bai sani ba shine, yanzu 'yan Najeriya idon su ya budewar da baza azo a yaudaresu da kudi ba, kuma 'yan Najeriya aiki suke bukata, saboda haka ba makawa PDP zata cinye zaben 2019 muddin mun fitar da dan takara wanda ya cancanta, kuma mutane suke kaunar sa," inji sakataren jam'iyyar ta PDP.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel