Rikicin Makiyaya: Mutane 7 sun Mutu a Benue

Rikicin Makiyaya: Mutane 7 sun Mutu a Benue

- Har yanzu ana jika game da matsalar tsaro a jihar Benue

- Rikicin Maharan Makiyaya na cigaba da zama hanyar salwantar rayuka a jihar

- Harin baya-bayan nan da aka kai a jiya ya janyo Mutuwar Mutane bakwai

Shugaban karamar Kwande ta jihar Benue Terdoo Kenti, ya tabbatar da Mutuwar Mutane bakwai tare da samun raunuka da karin wasu Mutane shida su kayi tun bayan da wadansu da ake zargin Makiyaya ne suka kai musu hari.

Rikicin Makiyaya: Mutane 7 sun Mutu a Benue

Rikicin Makiyaya: Mutane 7 sun Mutu a Benue

Terdoo ya tabbatar da hakanne ta wayar salula a garin Makurdi, sannan ya ce Maharan sun yi awan gaba da wata Mata yayin da suka kawo harin a daren jiya Asabar a kauyen Tseadough dake Mbachom a mazabar Yaav, yankin da ‘yan kabilar Tiv suke da yawan gaske a jihar ta Benue.

KU KARANTA: Sunayen ‘yan ta’addan da ‘yan sanda ke zargin Bukola Saraki da daukan nauyin aiyukan su

Sannan ya kara da cewa, Maharan sun kona gidaje masu yawa a yankin amma sai dai har ya zuwa yanzu basu kai ga gano ko su wanene suka kai harin ba kasancewar lokacin talatainin dare ne.

Kuma ya ce, tuni suka kai wadanda suka samu raunuka asibiti domin karbar magani tare kuma da kai gawar wadanda suka Mutu yayin iftila’in zuwa ma’ajiyar gawawwaki.

Daga karshe yayi kira ga Mutanen yankin da su kwantar da hankalinsu sannan kada su dauki doka a hannunsu balle suce zasu dauki fansa, a cewarsa tuni an sanar da hukumomin tsaro tare da duk masu fada aji faruwar lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel