Wani dan majalisa kuma na hannun daman gwamna Wike ya fita daga PDP, ya koma APC

Wani dan majalisa kuma na hannun daman gwamna Wike ya fita daga PDP, ya koma APC

Dan majalisar jihar Ribas nai wakiltar mazabar Ahoada ta Gabas, Martins Mannah, da aka zama a karkashin jam’iyyar PDP ya canja sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Mannah na hannun dama kuma na gaba-gaba a yakin neman zaben Gwamna Nyesom Wike a jihar Ribas, y ace ya fita daga jam’iyyar PDP ne saboda barazana da kakakin majalisar dokoki ta jihar da Gwamna Wike ke yi masa bayan ajiye shi gefe guda a harkokin gwamnati.

A jiya, Asabar ne, Mannah ya shiga jam’iyyar APC tare da magoya bayan sa 3000 a mazabar Ahoada ta Gabas, tare da bayyana cewar gwamnatin jihar bata sahale masa samun aiki ko daya bad a za a yi a mazabar sa cikin shekaru uku day a yi yana wakilcin jama’ar sa.

Wani dan majalisa kuma na hannun daman gwamna Wike ya fita daga PDP, ya koma APC

Gwamna Nyesom Wike

Da yake bayyana damuwar sa, Mannah ya ce, kasancewar jihar Ribas na jam’iyyar adawa na hana jihar samun aiyukan cigaba daga gwamnatin tarayya, tare da bayyana cewar akwai bukatar dinke Baraka tsakanin gwamnatin jihar da ta tarayya.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar APC ta dakatar da yakin neman zaben gwamna a jihar Ekiti, ta bayar da dalili

Sakon da nake so na mika ga jama’a ta shine; mun yiwa jam’iyyar PDP hidima da biyayya na tsawon shekara uku amma bamu ga wani cigaba ta fuskar cigaban kasa da al’umma ba. Da yawan mu a majalisar jiha ba ma jin dadin kasancewar mu ‘ya’yan jam’iyyar PDP kuma zamu koma APC tare da tabbatar da cewar PDP bata kara yin nasara a zaben 2019 dake zuwa ba,” a cewar Mannah.

Da yake nasa jawabin yayin karbar su, shugaban jam’iyyar APC a jihar Ribas, Ojukaye Flag-Amachere, ya dauki alkawarin cewar ba za a nuna masu banbanci ko mayar das u saniyar ware ba a harkokin jam’iyyar ta APC tare da bukatar su hada kai da jam’iyyar domin kayar da jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar na shekarar 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel