Maganar gaskiya shekaru 4 sun yi kadan da duk mai son ya kawo gyara a Najeriya - Osinbajo

Maganar gaskiya shekaru 4 sun yi kadan da duk mai son ya kawo gyara a Najeriya - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa a hakikanin gaskiya, shekaru hudu kacal sun yi kadan ga dukkan wani shugaba a Najeriya indai ana so ya kawo sahihin canji mai ma'ana a kasar.

Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabin sa na a wajen taron karawa juna sani da gidan jaridar nan na Financial Times ya shirya a garin Legas.

Maganar gaskiya shekaru 4 sun yi kadan da duk mai son ya kawo gyara a Najeriya - Osinbajo

Maganar gaskiya shekaru 4 sun yi kadan da duk mai son ya kawo gyara a Najeriya - Osinbajo

KU KARANTA: Kasar Ghana ta kakkabo jirgin karyar Jonathan

Legit.ng ta samu cewa mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa duk da kurarren lokacin da ke da akwai idan har kasa ta ci sa'a kamar yanzu da ta samu jajirtaccen shugaba, za ta iya samun cigaba sosai mai ma'ana.

A wani labarin kuma, Jam'iyyar mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) a jiya ta sanar da nada sabon Sakataren kwamitin taron gangamin ta watau National Convention Committee (NCC) biyo bayan murabus din da Sanata Benjamin Uwajumogu yayi a jiya.

Wanda zai maye gurbin sa, kamar dai yadda muka samu shine Sanata Victor Ndoma-Egba. Wannan dai na kunshe ne a cikin wani sakon kar-ta-kwana da jami'ain hulda da jama'a na jam'iyyar ta APC Malam Bolaji Abdullahi ya fitar a shafin sa na Tuwita.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel