Karuwai sun koka bisa rashin ciniki saboda Azumi a wata jihar da ake shari’ar Musulunci a Arewa

Karuwai sun koka bisa rashin ciniki saboda Azumi a wata jihar da ake shari’ar Musulunci a Arewa

- Kowacce sana'a na da yanayin karancin ciniki, hakan ce ta faru da Mata masu zaman kansu

- Matan sun bayyana irin asarar da suke tafkawa tun bayan fara Azumi

- Hakan ta sanya wasunsu har fara hijira zuwa makwabtan jahohi domin Kano tayi zafi

Mata masu zaman kansu a jihar Kano sun bayyana fuskantar karancin ciniki sakamakon shigowar Azumin Ramadan. Wannan halin rashin samun abokan huldar tasu ya jawo wasu ma har sun koma wasu jahohin domin Kanon tayi musu zafi.

Karuwai sun koka bisa rashin ciniki saboda Azumi a wata jihar da ake shari’ar Musulunci a Arewa

Karuwai sun koka bisa rashin ciniki saboda Azumi a wata jihar da ake shari’ar Musulunci a Arewa

Bayan gudanar da Azumi da ake kuma ‘yan Hisba da aka hukuma ta dorawa alhakin hani ga aikata munanan aiyuka a jihar ta matsa kaimi wajen kara takura musu ta hanyar kama su a duk sanda sukai arba.

Karuwai sun koka bisa rashin ciniki saboda Azumi a wata jihar da ake shari’ar Musulunci a Arewa

Karuwai sun koka bisa rashin ciniki saboda Azumi a wata jihar da ake shari’ar Musulunci a Arewa

A wani bincike da Jaridar Tribune ta gudanar a wuraren da su kayi kaurin suna wajen samun Mata masu zaman kansu irinsu Abbedie, Enugun, Wari, Hsysaws, BUK Lodge, da kuma Titin Bompai ya nuna cewa Matan kawai gararanbarsu suke.

KU KARANTA: Wani Sabon Hari ya salwantar da Rayukan Mutane 15 a Jihar Zamfara

Amma koda wata kuda ta hango wakilin Jaridar da yaje domin hada rahoto, nan take ta taho da sauri domin ko zata samu ya zama abin hulda da zata karu da shi. Sai dai taki yarda tayi Magana har sai da yayi mata ‘yar karamar siyayya

Dole ce ta saka ni shiga cikin wannan sana’ar, na taba Aure har ina da ‘ya’ya hudu. Amma bayan Mutuwar Miji na sai ya zamana babu mai daukar nauyinmu, hakan ta sanya dole na fara wannan harkar domin biyawa kaina da ‘ya’ya bukata." Yarinyar mai suna Joy ta amsa tambayar da majiyarmu tayi mata.

Amma koda aka tambaye ta dalilin rashin fitowarsu da yawa kuwa, cewa tayi “Tun bayan fara Azumi yawancin Abokan cinikayyar tasu suka daina zuwa, wanda hakan kuma ya bamu matsala mutuka wurin raguwar ‘yan kudaden da muke samu. A dalilin haka ma wasunmu har sun kaura zuwa wasu jahohin.” Joy ta bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel