Da dumin sa: allah ya yiwa tsohon Alkali kuma shugaban ICPC na farko rasuwa

Da dumin sa: allah ya yiwa tsohon Alkali kuma shugaban ICPC na farko rasuwa

Tsohon shugaban kotunan daukaka kara na Najeriya kuma shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatan gwamnati (ICPC), Mustapha Akanbi, ya mutu.

Akanbi ya mutu ne yau da misalign karfe 1:00 na dare a garin Ilorin ta jihar Kwara kamar yadda daya daga cikin ‘ya’yan sa, Barista Kabir Akanbi, ya sanar da jaridar The Nation.

Akanbi, ya rasu yana da shekaru 85 a duniya, sanna za a yi jana’izar sa idan anjima.

An haifi Akanbi ne ranar 11 ga watan Satumba na shekarar 1932 a garin Accra na kasar Ghana inda ya halarci makarantun firamre da sakandire har kuma ya fara aiki.

Da dumin sa: allah ya yiwa tsohon Alkali kuma shugaban ICPC na farko rasuwa

Marigayi Mustapha Akanbi

Bayan ya dawo Najeriya ya yi aiki a ma’aikatar ilimi, sashen yada labarai kafin daga bisani ya samu tallafin gwamnati ya karanta ilimin shari’a a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria kafin daga bisani ya zurafafa karatun sa na shari’a a Turai.

Ya zama lauya a Turai a shekarar 1963 sannan ya shiga sahun lauyoyin Najeriya a shekarar 1964, a watan Janairu.

DUBA WANNAN: Ganduje ya yi kaca-kaca da Kwankwaso a kan fitar da daliabai waje, ya ce damfara ce kawai

A shekarar 2000 ne tsohon shugaban kasa Obasanjo ya nada Akanbi a matsayin shugaban hukumar ICPC na farko.

Akanbi, ya kasance daya daga cikin dattijan Najeriya da ake girmamawa kuma ake daukan maganar sa da muhimammanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel