Jam’iyyar APC ta dakatar da yakin neman zaben gwamna a jihar EKiti

Jam’iyyar APC ta dakatar da yakin neman zaben gwamna a jihar EKiti

- Jam’iyyar APC mai mulki ta dakatar da yakin neman zaben dan takarar ta na gwamna a jihar Ekiti, Kayode Fayemi

- Jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne bayan harbin da aka yi a wurin taron da aka shiryawa Fayemi ranar juma’a kamar yadda shugaban ta a jihar, Jide Awe, ya sanar

- Mista Awe ya kafe kan cewar, dan bindigar ya yi niyyar halaka dan takara jam’iyyar APC ne, Fayemi, amma sai harsashin ya sami wani daban

Jam’iyyar APC mai mulki ta dakatar da yakin neman zaben dan takarar ta na gwamna a jihar Ekiti, Kayode Fayemi, da aka shirya farawa gobe, Litinin.

Jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne bayan rundunar ‘yan sanda a jihar ta fitar da sakamakon harbin da aka yi a wurin taron da aka shiryawa Fayemi ranar juma’a kamar yadda shugaban jam’iyyar a Ekiti, Jide Awe, ya sanar da manema labarai a Ado Ekiti, babban birnin jihar.

Jam’iyyar APC ta dakatar da yakin neman zaben gwamna a jihar EKiti

Dakta Kayode Fayemi

Wani dan sanda da wasu rahotanni suka bayyana cewar na bogi ne, ya yi harbi a tare da samun Opeyemi Bamidele, tsohon mamba a majalisar wakilai, yayin gangamin taron yakin neman zaben Fayemi na ranar juma,a.

DUBA WANNAN: Ganduje ya yi kaca-kaca da Kwankwaso a kan fitar da dalibai karatu waje, ya ce karya ce da damfara kawai

Mista Awe ya kafe kan cewar, dan bindigar ya yi niyyar halaka dan takara jam’iyyar APC ne, Fayemi, amma sai harsashin ya sami Bamidele.

Awe, ya bukaci jami’an ‘yan sanda das u gudanar da bincike mai zurfi tare da bayyana sakamakon binciken su ga jama’a.

Saidai jam’iyyar ta APC tayi watsi da sakamakon farko da hukumar ‘yan sanda ta fitar dake nuna cewar an yi harbin ne bisa kuskure, bad a gan-gan ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel