Wani Sabon Hari ya salwantar da Rayukan Mutane 15 a Jihar Zamfara

Wani Sabon Hari ya salwantar da Rayukan Mutane 15 a Jihar Zamfara

Kamar yadda kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito mun samu rahoto cewa, an tafka asarar rayukan mutane a wani mummunan hari da ya afku a yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya.

Bayan kimanin mako guda da kisan rayukan Mutane 26 na al'ummar Najeriya a yankin Arewa maso Yammacin jihar Zamfara, wasu 'yan bindiga sun sake kai hari wani kauye cikin jihar inda suka salwantar da rayukan mutane 15 a ranar Juma'ar da ta gabata.

Kakakin hukumar 'yan sanda na Jihar, DSP Muhammad Shehu, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Asabar din da ta gabata a Birnin Jihar na Gusau.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan hari ya afku ne yayin da wasu 'yan ta'adda suka kai hari kan al'ummar kauyen Zakuna dake cikin Karamar hukumar Anka ta jihar.

Wani Sabon Hari ya salwantar da Rayukan Mutane 15 a Jihar Zamfara

Wani Sabon Hari ya salwantar da Rayukan Mutane 15 a Jihar Zamfara

Rahotanni sun bayyana cewa Jihar Zamfara na ci gaba da shan fama da miyagun hare-hare a cikin kwanakin nan inda rayukan dumbin al'umma suka salwanta.

DSP Shehu ya bayyana cewa, maharan sun kai farmaki ne kauyen Zakuna da sanyin safiyar ranar 1 ga watan Yuni inda suka yi awon gaba da wasu shanu na al'ummar kauyen.

KARANTA KUMA: Lai Muhammad ya bayyana amincin sa dangane da shirin Najeriya na daukar nauyin taron UN

A cewar sa, a yayin da wata ƙungiyar tsaro ta sa kai ta kalubalancin wannan barayin shanu da ya sanya suka arce, sai kuma suka mayar da martani da daura damara ta kai hari kan al'ummar kauyen inda suka salwantar da rayukan mutane 15 nan take.

Shehu ya ci gaba da cewa, kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mista Kenneth Ebrimson, ya bayar da umarnin gudanar da bincike na diddigi domin bankado masu hannu cikin wannan ta'addanci.

A yayin haka kuma, babban jami'in dan sanda ya mika kokon barar sa ga al'ummar jihar akan tallafawa hukumar da rahotanni da za su taimaka kwarai da aniyya wajen magance kalubalen tsaro a fadin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel