'Yan sanda sun tabbatar da wani sabon Hari kan Al'ummar Jihar Filato

'Yan sanda sun tabbatar da wani sabon Hari kan Al'ummar Jihar Filato

Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da afkuwar wani sabon hari a ranar Asabar din da ta gabata kan al'ummar yankin Kura dake gundumar Gashish a karamar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato inda wasu 'yan bindiga suka salwantar da rayukan mutane uku.

A ranar Asabar din da ta gabata ne Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, ASP Terna Tyopev, shine ya tabbatar da wannan lamari yayin ganawa da manema labarai a babban birnin Jihar na Jos.

A cewar kakakin, wannan hari ya afku da tsakar daren ranar Juma'a da kuma safiyar ranar Asabar din da ta gabata.

'Yan sanda sun tabbatar da wani sabon Hari kan Al'ummar Jihar Filato

'Yan sanda sun tabbatar da wani sabon Hari kan Al'ummar Jihar Filato

Yake cewa, "mun samu wannan rahoto ne da misalin karfe 7.00 na safiyar ranar Asabar da cewar wasu 'yan bindiga sun kai hari kan al'ummar Kura da misalin karfe 9.30 na daren jiya."

KARANTA KUMA: Lai Muhammad ya bayyana amincin sa dangane da shirin Najeriya na daukar nauyin taron UN

Legit.ng ta fahimci cewa mutane uku ne suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon wannan hari da ya afku, inda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bayyana suneyen su kamar haka; Dawala Bullet mai shekaru 30, Fidelis Richard mai shekarau 31 da kuma Iliya Doro mai shekaru 60 a duniya.

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa, tuni jami'an hukumar suka fara gudanar da bincike wajen bankado masu hannu cikin wannan aika-aikata domin su fuskanci fushin doka mai adalci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel