Sojin Najeriya sun aike da 'yan Boko Haram 10 Lahira, sun kwato miliyoyin naira

Sojin Najeriya sun aike da 'yan Boko Haram 10 Lahira, sun kwato miliyoyin naira

- Rundunar Operation Lafiya Dole da ke yaki da 'yan Boko Haram a sun sami babban Nasara

- Sojojin sun kashe 'yan Boko Haram 10 a samame daban-daban da suka kai sansanin 'yan ta'adan

- Sun kwato makamai, wayoyin tafi da gidanka da kuma zunzurutun kudi fiye da naira miliyan 2

Dakarun sojin Najeriya sunyi nasara halaka 'yan ta'adda guda 10 a wanni samame da suka kai a kauyen Ngelkona da ke karamar hukumar Ngala a jihar Borno.

Kwamandan rundunar Operation Lafia Dole Col. Onyeama Nwachukwu ne ya sanar da hakan a garin Maiduguri inda ya ce Sojin Najeriyan na rundunar 153 sun sami nasara tare da taimakon sojin Kamaru.

An kashe da ma'ajin Boko Haram, ku duba milyoyin kudin da aka samu wajen shi

An kashe da ma'ajin Boko Haram, ku duba milyoyin kudin da aka samu wajen shi

Sojin sunyi raga-raga da 'yan ta'adan kuma suka kwace bindigogi kirar AK 47 guda biyu da tutar Boko Haram da wayar salula tare kuma da fasfo din kasar Kamaru.

KU KARANTA: Dubi yadda jihohin Arewa ke kan gaba wajen adadin mutanen da za'a dauka aikin 'Dan sanda

A wato samamen da dakarun bataliyar 82 na Operation Lafiya Dole suka kai a kauyen Ngoshe da karamar hukuma Gwoza, sojin sun kashe dan ta'ada guda daya kuma sun sami AK 47 guda daya da alburusai da kuma bam guda hudu.

An kashe da ma'ajin Boko Haram, ku duba milyoyin kudin da aka samu wajen shi

An kashe da ma'ajin Boko Haram, ku duba milyoyin kudin da aka samu wajen shi

Har ila yau, dakarun bataliya ta 27 da suka tafi wata sintiri a jiya Juma'a sun kai samame a sansanin Boko Haram da ke dajin Yarididi da ke karamar hukumar Geidam na jihar Yobe.

"A yayin da suka sai samamen, sojojin sun bude wuta a kan yan ta'adan wanda hakan ya sa suka tsere da raunukar harsasai kuma suka bar zunzurutun kudi tare da wasu kayayakin," inji shi.

An kashe da ma'ajin Boko Haram, ku duba milyoyin kudin da aka samu wajen shi

An kashe da ma'ajin Boko Haram, ku duba milyoyin kudin da aka samu wajen shi

Ya kuma kara da cewa dakarun sojin sun samo AK 47 guda uku, alburusai mai carbi guda 21 tare da babur guda daya da wayar salula guda biyu.

A cewarsa, dakarun sojin sun kamo kudi N2,280,000 miliyan daga mabuyar yan ta'adan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel