Wani Malamin Jami'a ya bayar da Shawarar zartar da Hukuncin Kisa kan masu Safara da Fatauci Muggan 'Kwayoyi

Wani Malamin Jami'a ya bayar da Shawarar zartar da Hukuncin Kisa kan masu Safara da Fatauci Muggan 'Kwayoyi

Wani Malamin Jami'a Dakta Bala Muhammad, ya bayar da shawarar sa ta zartar da hukuncin Kisa kan Dilolin Muggan Kwayoyi a Kasar nan inda yake ganin hakan zai magance annobar ta'ammali da Muggan kwayoyi dake ci gaba da faskara a tsakanin Matasa.

Dakta Muhammad wanda Malami ne a Jami'ar Bayero dake Jihar Kano yayi wannan kira ne a ranar Asabar din da ta gabata, yayin wata Laccar Azumin Ramadana ta musamman da Cibiyar Musulunci ta Najeriya ta dauki nauyin gudanarwa a Jami'ar.

Yake cewa, fataucin Muggan Kwayoyi a Kasar nan ta Najeriya ya kai wani munzali na kaico da damuwa, wanda ke barazana ga Matasa na jefa cikin hadurran daidaita rayuwar su.

A sanadiyar haka ne babban Malamin ya bayyana cewa, hanyar magance wannan kalubale itace zartar da hukuncin mai girman gaske kan masu safara da fataucin Muggan Kwayoyi a Kasar nan.

Ya kirayi al'ummomin Kasar nan akan su tursasa wakilan su dake Majalisar Dokoki ta Tarayya wajen dabbaka shawarar sa ta zartar da hukuncin mai girman gaske akan masu aikata laifukan da suka shafi Muggan Kwayoyi.

Wani Malamin Jami'a ya bayar da Shawarar Hukuncin Kisa kan masu ta'ammali da Fatauci Muggan 'Kwayoyi

Wani Malamin Jami'a ya bayar da Shawarar Hukuncin Kisa kan masu ta'ammali da Fatauci Muggan 'Kwayoyi

A yayin haka kuma, wani Malami na Jami'ar cikin na sa gabatar da jawaban, Bashir Adamu ya bayyana cewa ta'ammali da Muggan Kwayoyi yana da nasaba ne da raunin Imani a tsakankanin Matasan Kasar nan.

Ya kuma bayyana yadda mummunan tasirin abokai ke taka rawar gani wajen haddasa ta'ammali da Muggan Kwayoyi a tsakanin Matasa tare da yadda wasu Iyayen ke gazawa wajen rashin bayar da muhimmiyar kulawa da tarbiyar Yaran da suka haifa.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Jihar Kano ta matsa Lamba akan yaki da Maganin Tari na Codeine

Mallam Adamu ya kuma zargi yadda ta'mmali da Muggan kwayoyi ke ci gaba da karuwa a tsakanin Mata a sakamakon cin zarafi da kuma keta masu haddi a kasar nan.

A sanadiyar haka ne Malaman Jami'ar su ke kira dangane da a tashi farka domin tunkara gami da magance wannan barazana inda suke lamarin na Mu duka ne.

Legit.ng ta fahimci cewa, Malaman sun tofa albarkacin bakunan su ne a Lacca ta musamman mai take: "Barazanar Muggan Kwayoyi; Ina Mafita" da aka gudanar kamar yadda kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel