Yanzunnan: Sakataren babban taron APC ya sauka daga mukaminsa

Yanzunnan: Sakataren babban taron APC ya sauka daga mukaminsa

- Senator Benjamin Uwajumogu, na All Progressives Congress (APC) yayi murabus

- Shine sakataren National Convention Committee da ke duba hada-hadar yiwuwar taron su na kasa

- Ya bayyana dalilansa kamar haka:

Yanzunnan: Sakataren babban taron APC ya sauka daga mukaminsa

Yanzunnan: Sakataren babban taron APC ya sauka daga mukaminsa

Kamar yadda Godson Amadikwa yasa hannu, sakataren shi, yace yanke shawarar da kwamitin yayi na ya ajiye aiki ya biyo bayan dalilan shi na kanshi kuma kuma cigaban jam'iyyar APC a jihar Imo.

Ajiye aikin sanata Benjamin Uwajumogu ya biyo bayan shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Chief John Odigie-Oyegun yace bazai nemi zarcewa ba a taron jam'iyyar na kasa da za'ayi a 23 ga watan yuni 'a ra'ayin jam'iyyar'.

Odigie-Oyegun ya sanar a ranar juma'a da dare a Abuja, cewa ya yanke shawara ne bayan ya nemi Jin ra'ayin makusantan shi a siyasa da kuma iyalanshi. Amma ba wai don yaji tsoro ba.

Ya kara da cewa kwamitin aiyuka na kasa an tsawaita musu lokacin lokacin mulkin su wanda kwamitin zababbun jam'iyyar na kasa suka fuskanci ci baya sakamakon adawar ra'ayi daga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

DUBA WANNAN: An kama wanda yayi kokarin kashe Fayemi

Yace tsawaita wa'adin mulkin zai saisaita jam'iyyar kuma ya hana hayaniyar da take fuskanta a kwanakin nan.

Odigie-Oyegun ya jawo hankalin shuwagabannin jam'iyyar dasu maida jam'iyyar kakkarfa domin fuskantar zaben 2019.

"Yanzu da kwamitin taron ya bukaci yan takara da su siya fom din takarar kujerun, ya zama dole in fadi matsayina."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel