Sharudda 4 da Saraki, Dogara Da su Kwankwaso suka gindaya domin cigaba da zama a APC

Sharudda 4 da Saraki, Dogara Da su Kwankwaso suka gindaya domin cigaba da zama a APC

- Yayin da shekarar zaben gama gari na 2019 ke ta kara karatowa, siyasa a kasar na ta kara daura damarar su domin fuskantar zaben da ake ganin zai kasance cike da tarihi.

- Wannan ne ma ya sanya kawo yanzu tuni lamurra suka fara daukar zafi musamman ma a tsakanin fitattun jam'iyyun kasar na APC mai mulki da kuma PDP ta adawa.

Legit.ng ta samu cewa tuni dai wani bangare daga jam'iyyar APC din da suka bar jam'iyyar PDP a gabanin zaben 2015 suka fara wani yunkurin ballewa daga jam'iyyar.

Sharudda 4 da Saraki, Dogara Da su Kwankwaso suka gindaya domin cigaba da zama a APC

Sharudda 4 da Saraki, Dogara Da su Kwankwaso suka gindaya domin cigaba da zama a APC
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Idan na zama Gwamna zan tura Fayose gidan yari - Fayemi

Sai dai mun samu cewa jagororin bangarorin biyu sun yi wata ganawa a makon da ya gabata inda aka yanke shawarar kafa wani kwamitin da zai lalubo hanyar sasanci a tsakanin su.

Daga baya ne ma muka samu cewa bangarin na sabuwar PDP sun zayyana sharuddan su 4 da suke so a cika masu kafin su zauna a jam'iyyar:

1. Janye kararrakin da aka shigar a kan Sanata Abubakar Bukola Saraki.

2. Bai Honorable Yakubu Dogara da Dr Rabiu Musa Kwankwaso wasu kujeru a zaben shugabannin jam’iyyar APC a jihohinsu.

3. Kawo karshen muzgunawa da EFCC ke yi wa wasu daga cikinsu.

4. Sa sufeto Janar na ‘yan sanda da ya gurfana gaban majalisar dattawa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel