Ta tonu: 'Yan ta'addan Boko Haram sun bullo da sabuwar hanyar kaddamar da kunar bakin wake

Ta tonu: 'Yan ta'addan Boko Haram sun bullo da sabuwar hanyar kaddamar da kunar bakin wake

Hukumar rundunar jami'an tsaron leken asiri ta tarayyar Najeriya watau Department of State Services, DSS ta sanar da samun nasarar bankado wasu sabbin dabarun da 'yan ta'addan Boko Haram suka bullo da su na kaddamar da hare-haren kunar bakin wake a kasar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata takardar sirri da hukumar ta aike wa kwamandan rundunar sojojin Najeriya dake a garin Yola babban birnin jihar Adamawa a shiyyar Arewa maso gabashin kasar.

Ta tonu: 'Yan ta'addan Boko Haram sun bullo da sabuwar hanyar kaddamar da kunar bakin wake

Ta tonu: 'Yan ta'addan Boko Haram sun bullo da sabuwar hanyar kaddamar da kunar bakin wake

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya ta rasa kwamandojin ta 5 a garin Gwoza

Legit.ng ta samu cewa a cikin wasikar, jami'an leken asirin sun bayyana cewa yanzu 'yan kungiyar na Boko Haram sun soma anfani ne da tsaffin mutane kama daga shekaru 50 zuwa 60 domin kaddamar da harin da nufin badda kamar su.

Haka zalika wasikar ta kara fayyace cewa duk dai a cikin sabuwar dubarar, tsaffin za su nade kansu da boma-bomai sannan kuma su kwanta suyi kamar marasa lafiyar da aka kai wa hari a kusa da shingayen jami'an tsaro da nufin su tara jama'a kafin daga bisani su tarwatsa kan su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel