Kasar Ghana ta kakkabo jirgin karyar tsohon shugaban Najeriya Jonathan

Kasar Ghana ta kakkabo jirgin karyar tsohon shugaban Najeriya Jonathan

Babban jakadan kasar Ghana a Najeriya Mista Rashid Bawa ya nesanta kasar sa da kalaman da aka ruwaito wai cewa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce shugaban kasar Ghana Nana Akuffo-Addo ne ya fada game da harkar tsaron Najeriya.

Da yake karin haske game da lamarin, jakadan kasar Ghana din ya fada a ranar Juma'ar da ta gabata cewa tsohon shugaban kasar ya datsi kalaman shugaban kasar ta Ghana ne amma ba haka yake nufi ba.

Kasar Ghana ta kakkabo jirgin karyar tsohon shugaban Najeriya Jonathan

Kasar Ghana ta kakkabo jirgin karyar tsohon shugaban Najeriya Jonathan

KU KARANTA: Yadda wani matashi ya kwaso Kanjamau a Fesbuk

Legit.ng ta tuna cewa a kwanan baya tsohon shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana takaicin sa akan yadda yace wasu bata gari 'yan asalin kasar nan suka bata sunan kasar a idanun duniya ta hanyar aikata munanan laifuka.

A kokarin sa na yin karin bayani game da hakan, Goodluck Jonathan ya bayar da misalin yadda yace shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo ya yi anfani da kasar ta Najeriya wajen bayyana yadda harkoki ke cigaba da tabarbarewa musamman ma a fannonin tsaro da tattalin arziki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel