Gangancin tuki ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 6 da raunata wasu 11

Gangancin tuki ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 6 da raunata wasu 11

- A kalla mutane 6 ne suka rasu a wata mummunan hatsarin mota da ya faru a jiya Alhamis 31 ga watan Mayu a karamar hukumar Oru na jihar Imo

- Kimanin mutane 11 sun jikatta sakamakon mummunnan hatsarin motan

- Hukumar kiyaye haddura na kasa FRSC sun alakanta afkuwar hadarin da tukin ganganci da wani direban Tipa ya yi

Hukumar kiyaye haddura na kasa (FRSC) ta bayyana cewa rashin bin dokokin tuki da wani direban tipa kirar Marsandi 611 ne ya janyo afkuwar wata mummunan hatsarin mota da ya yi sandiyar mutuwar mutane shida a karamar hukumar Oru ta gabas da ke jihar Imo da ya faru a ranar Alhamis 31 ga watan Mayu.

Wani mummunan hatasarin mota ya lakume rayuka 6, wasu mutane 11 sun jikkata

Wani mummunan hatasarin mota ya lakume rayuka 6, wasu mutane 11 sun jikkata

Kwamandan hukumar FRSC na jihar Imo, Joseph Aremu ya tabbatar da afkuwar hadarin yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Asabar 2 ga watan Yuni a garin Owerri. Ya ce mutane 17 ne hadarin ya ritsa da su.

KU KARANTA: Baya ga lalata huhu, likitoci sun gano wasu manyan illoli da tabar cigari ke yiwa dan-adam

Aremu ya ce a cikin fasinjojin guda 17 da hatsarin ya ritsa da su, shidda sun riga mu gidan gaskiya, yayinda wasu 11 sun samu munanan raunuka kuma tuni jami'an FRSC din sun garzaya da su asibiti.

Ya ce binciken da hukumar ta fara gudanarwa ya nuna cewa direban tipper kirar Marsandi ne ya janyo hadarin saboda ya saba dokokin tuki a hanya.

Aremu ya ce hukumar ta fara zurfafa bincike a kan hatsarin kuma ya kara da cewa zai ziyarci kungiyar direbobin tipper na jihar don jin ba'asi.

Ya yi alkawarin cewa hukumar za ta fara sanya idanu a kan direbobi masu karya dokokin tuki tare da hukunta su kamar yadda doka ya tanada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel