Fitaccen dan siyasa a Abuja ya sha da kyar hannun matasa don ya nuna goyon bayan sa ga tazarcen Buhari

Fitaccen dan siyasa a Abuja ya sha da kyar hannun matasa don ya nuna goyon bayan sa ga tazarcen Buhari

Labarin da muka samu daga majiyar mu ta DailyTrust ta bayyana mana cewa a jiya ne dai fitaccen dan siyasar nan kuma shugaban karamar hukumar Kuje dake a birnin tarayya Abuja Alhaji Abdullahi D. Galadima tare da mataimakin sa Mista Samuel Tanko sun sha da kyar a hannun mafusatan matasa.

Haka ma kuma kamar dai yadda muka samu mafusatan matasan sun yi kukan kura sun afkawa shugabannin karamar hukumar ne biyo bayan nuna goyon bayan su ga takarar tazarcen shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Fitaccen dan siyasa a Abuja ya sha da kyar hannun matasa don ya nuna goyon bayan sa ga tazarcen Buhari

Fitaccen dan siyasa a Abuja ya sha da kyar hannun matasa don ya nuna goyon bayan sa ga tazarcen Buhari

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya tayi rashin kwamandojin ta 5 a Borno

Legit.ng ta samu cewa matasan dai sun farwa shugabannin karamar hukumar ne yayin da suke fita daga dakin taro jim kadan bayan kammala tattaunawar su da sauran jiga-jigan jam'iyyar masu rike da mukamai.

A wani labarin kuma, Tsohon babban na hannun damar shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari kuma fitaccen dan adawa Injiniya Buba Galadima ya bayyana cigaba da tsare jagoran 'yan shi'a a Najeriya Ibrahim Zakzaky da gwamnatin tarayya ke ci gaba dayi a matsayin rashin adalci tsagwaron sa.

Injiniya Buba Galadima ya bayyana hakan ne a yayin da ake fira da shi a gidan talabijin mai zaman kan sa na AIT a wani shiri da ake cewa "Focus Nigeria: Matters Arising" lokacin da aka tambaye shi ra'ayin sa game da cigaba da tsare shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel