Ina tsoron makudan kudin da yan adawa suka tara don kada ni a 2019 - Shugaba Buhari

Ina tsoron makudan kudin da yan adawa suka tara don kada ni a 2019 - Shugaba Buhari

- Anyi taron dangi domin tumbuke shugaba Buhari daga karagar mulki a 2019

- Ga alama masu adawa sun fi masu mulki kudin kashewa don yakin neman zabe

- A baya shugaban ya sami kudi daga talakawa, yanzu kuwa, ba lallai su baiwa mai mulki kudi ba

Ina tsoron makudan kudin da yan adawa suka tara don kada ni a 2019 - Shugaba Buhari

Ina tsoron makudan kudin da yan adawa suka tara don kada ni a 2019 - Shugaba Buhari

A jawabin shugaba Buhari ga masoya, yayin da 'yan kungiyar BSO suka kai masa a Asor Rock, yace yana tsoron jam'iyyun adawa da masu goya musu baya sunfi karfin jam'iyyarsa ta fannin kayan aiki da ka iya kayar dashi a zabe mai zuwa.

Zaben 2019 din dai saura baifi wata 9 ayi shi ba, kuma shugaban yana neman takara a zango na biyu zuwa 2023.

A cewarsa, ina tsoron ko jam'iyyarmu ta APC tana da kudin da zamu iya aikin yakin zabe dasu, domin masu adawa sunfi mu kudi, kuma sun tara kudade makudai don aikin yakar mu lokacin kamfe.

A baya dai, babau mulki a hannun APC amma talakawa suka yi karo-karo suka kaya da gwamnati da kudadensu da jajircewarsu, sai dai kamar a wannan karon, babu wannan karsashi daga bangaren talakka, wanda bai ji a aljihu ba ya zuwa yanzu duk da an kusa gama mulkin.

DUBA WANNAN: JAmmeh yayi karyar warkar da kanjamau

Jam'iyyar PDP dai ta mayar wa da shugaba Buhari martani, inda tace ai duk shure-shure ne wanda baya hana mutuwa, tsoron shugaban na faduwa zabe ne domin canjin sa ya zo wa jama'a da wahala da kangin talauci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel