An kulle wani maigidan haya da ya kulle mai-haya cikin gida kan kudin haya

An kulle wani maigidan haya da ya kulle mai-haya cikin gida kan kudin haya

- Rigimar haya da biyan kudinta kan kai ga kotu a wannan zamani na talauci

- Ya kulle su a cikin gida saboda sunki biyansa kudin haya

- Yanzu kam shima kotu ta kulle shi na dan lokaci

An kulle wani maigidan haya da ya kulle mai-haya cikin gida kan kudin haya

An kulle wani maigidan haya da ya kulle mai-haya cikin gida kan kudin haya

Oyetunji Oyebode, mai bada hayar gidaje a jihar Legas, ya gamu da fushin kotu, bayan da ya kulle wata mai haya a gidansa a dakinta, bisa dalilin wai taki biyansa kudin haya kuma taki tashi daga gidan.

Wadda ya kulle din, tace ta biya shi kudin haya, sannan ta jira ya gyara mata rufin dakin da yake yoyo da damina, da yaqi, sai ta gyara da kudinta, amma ta sanya aniyar zata cire a kudin haya na shekara mai kamawa, wanda hakan tayi.

DUBA WANNAN: An kama wadanda suka kai hari kan dan takara a Ekiti

Shi kuwa gogan naka, da ya gaji da bibiiyar kudin hayarsa, sai kawai ya rufe ta cikin daki da kwado, bayan ya san tana ciki, wanda hakan ya janyo hadari ga rayuwarta.

Kotu ta kulle shi bisa kokarin tada husuma, tayar da fitina, da kokarin karfa-karfa, a gidan yari, na wucin gadi, shima yaji yadda ake ji.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel