An cafko wanda ya kai harin bindiga kan Ministan Buhari a jiharsa

An cafko wanda ya kai harin bindiga kan Ministan Buhari a jiharsa

- Fayemi ya je jiharsa takarar gwamna bayan ajje aiki a makon jiya

- An sami wanda ya kai harbin kuma an gani ashe dansanda ne

- Harbin nasa ya sami wani hwanarabul dake zaune a taron

An cafko wadanda suka kai harin bindiga kan Ministan Buhari a jiharsa

An cafko wadanda suka kai harin bindiga kan Ministan Buhari a jiharsa

A kame da ya kankama na kujerar gwamna da za'a yi a watan gobe, yakin cacar baka tsakanin APC mai adawa da PDP mai mulki a karamar jihar Ekiti ya kai an fara harbe harbe. inda wani kurtun dansanda da aka haya ya harbo harsasai kan gungun 'yan APC.

Harbin dai ya sami wani tsohon dan majalisar tarayya daga jihar wanda ke zaune a taron amma bai sami tsohon gwamna kuma tsohon minista Fayemi ba.

Hukumar Yansandar jihar, ta saki sunan wanda yayi harbin da cewa kurtu ne na dansanda, kuma an kama shi an kai Legas domin fuskantar hukunci.

Dansandan ya karbi kudi ne daga wani dan siyasa domin aikin harin nasa, kuma bama a jihar yake aiki ba.

DUBA WANNAN: Ta kashe mijinta bayan ya mata duka

Jam'iyyar APC dai ta ce gwamnatin Fayose ce ke son ganin bayan Fayemi, shi yasa ta kitsa harin, shi kuwa tsohon ministan ko gezau.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel