Daga karshe: Oyegun ya fadi dalilin da yasa ba zai sake tsayawa takara ba

Daga karshe: Oyegun ya fadi dalilin da yasa ba zai sake tsayawa takara ba

- Ciyaman din jam'iyyar APC, Cif John Odigie-Oyegun ya bayyana dalilin da yasa ya janye daga sake tsayawa takara

- Oyegun ya ce ya yi shawara da iyalansa da abokansa kafin ya yanke shawarar janyewar don yana ganin hakan zai fi zama alheri ga jam'iyyar

- Ya kuma kara da cewa janyewarsa zai magance wasu matsaloli da ke tasowa a jam'iyyar da ka iya raba kawunan mutane

Ciyaman din jam'iyyar APC na kasa, Cif John Odigie-Oyegun ya yi bayani a kan matakin da ya dauka na janyewa daka takarar shugabancin jam'iyyar da za'a gudanar a taron gangamin jam'iyyar da za'ayi nan gaba.

Ta tonu: Oyegun ya bayyana dalilin da yasa ba zai yi takarar shugabancin jam'iyyar APC da Oshiomole ba

Ta tonu: Oyegun ya bayyana dalilin da yasa ba zai yi takarar shugabancin jam'iyyar APC da Oshiomole ba

KU KARANTA: Tirkashi: 'Yan a ware na jam'iyyar APC a jihar Kaduna sun sake rabuwa gida biyu, sun fadi dalilinsu

A yayin da ya ke magana a daren jiya Juma'a a gidansa da ke Abuja, Ciyaman din jam'iyyar ya ce: "Yanzu da kwamitin shirya taron gangamin ta fara siyar da fom ga masu sha'awan takarar mukamai a jam'iyyar, ya zama dole in bayyana matsaya ta.

Na yi shawara sosai da iyalai na da abokai ne da kuma abokan aiki na. Duk da cewa ina da sha'awar sake tsayawa takarar ciyaman din jam'iyyar ta mu, na yanke shawarar zan janye saboda hakan zai fi zama alkhairi ga jam'iyyar".

Oyegun ya kara da cewa wannan matakin da ya dauka ba zai hana shi cigaba da bayar da gunmawarsa wajen cigaban jam'iyyar ba hasali ma ya yi hakan ne saboda yana ganin hakan zai taimaka wajen warware wasu matsololin da ke tasowa a jam'iyyar.

Duk da hakan ya ce zai cigaba da gudanar da ayyukansa a matsayin ciyaman din jam'iyyar har zuwa ranar 25 ga watan Yuli da za'a rantsar da sabbin shugabanin jam'iyyar.

A dai kwankin baya ne Legit.ng ta kawo muku rahoton inda wasu daga cikin 'ya'yan jam'iyyar na APC suka nuna goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomole don ya tsaya takarar ciyaman din jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel