Gwamnatin Jihar Kano ta matsa Lamba akan yaki da Maganin Tari na Codeine

Gwamnatin Jihar Kano ta matsa Lamba akan yaki da Maganin Tari na Codeine

Mun samu rahoton cewa gwamnatin jihar Kano ta shirya gagarumin yaki akan tsarkake al'umma da kewayen jihar ta daga dukkanin magungunan masu dauke da sunadarin Codeine.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, kwamitin kula da harkokin magunguna karkashin ma'aikatar lafiya ta jihar ta kaddamar da aikace-aikace na bibiyar shagunan sayar da magunguna da kuma daidaikun mutane domin kwace duk wani maganin mai sunadarin Codeine.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan shiri yana daya daga cikin manufofin gwamnatin jihar wajen tsarkake ta daga dukkan magunguna na kwayoyi da na ruwa masu dauke da sunadarin Codeine dangane da umarni da gwamnatin tarayya ta gindaya.

Gwamnatin Jihar Kano ta matsa Lamba akan yaki da Maganin Tari na Codeine

Gwamnatin Jihar Kano ta matsa Lamba akan yaki da Maganin Tari na Codeine

Jagoran wannan kwamiti, Abdu Umar Madaki, ya bayyana cewa sun ziyarci kimanin manyan kamfanoni 20 masu rarraba magunguna a jihar domin tsarkake su daga nau'ikan maganin tari mai sunadarin Codeine.

Mallam Abdu ya kirayi dukkanin kamfanonin da masu sayar da magungunan Codeine akan su hada gwiwa da ma'aikatar laafiya ta jihar wajen tsarkake jihar daga fataucin muggan magunguna masu kunshe da sunadarin Codeine.

KARANTA KUMA: Mutane 17m sun haure daga Nahiyyar Afirka domin Tafiya Cirani - UN

A yayin haka kuma, gwamnatin jihar ta bayar da tabbacin ta na hada gwiwa da hukumomin kula da magunguna da hana fataucin muggan kwayoyi gami da dukkanin masu ruwa da tsaki wajen tunkarar wannan annoba ta safara da ta'ammali da muggan kwayoyi a jihar

Rahotanni sun bayyana cewa watanni kadan da suka gabata ne gwamnati ta tsarkake jihar Kano daga muggan kwayoyi da kuma wadanda suka lalace tare da damke masu hannun cikin aikata wannan babban laifi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel