PDP ta barrantar da kanta daga ikirarin Orji Kalu na Kashe Abokan Adawa

PDP ta barrantar da kanta daga ikirarin Orji Kalu na Kashe Abokan Adawa

Jam'iyyar adawa ta PDP ta barrantar da kanta ta kalaman tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, wanda ya bayyana cewa mambobin jam'iyyar a wani sa'ilin su kan kawar da abokan adawar su daga doron Kasa domin cimma manufa ta siyasa.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, jam'iyyar ta tsarkake kanta ne daga wannan mummunan kalamai da sanadin kakakin ta, Mista Kola Ologbondiyan a yayin ganawa da manema labarai.

Mista Ologbondiyan ya kirayi tsohon gwamnan jihar Abia a kan ya fito karara domin yiwa kalaman sa fashin baki domin kuwa jam'iyyar PDP ba za ta alakantu da wannan lamari ba.

Cikin wani bidiyo a yayin taron ranar Alhamis na jiga-jigan jam'iyyar APC reshen Kudu Maso Gabas da aka gudanar a babban kasar nan na tarayya, Orji Kalu ya bayyana cewa, ya na da masaniyar 'yan siyasa su kan kawar da abokan adawar su daga doron kasa domin cikar burikan su na samun nasara a faggen siyasa.

PDP ta barrantar da kanta daga ikirarin Orji Kalu na Kashe Abokan Adawa

PDP ta barrantar da kanta daga ikirarin Orji Kalu na Kashe Abokan Adawa

A kalaman sa, "cikin kowace dimokuradiyya akan samu sa'insa da sabani. Mun saba kashe mutane a jam'iyyar PDP domin cimma manufofin mu wanda haka ba daidai bane."

Legit.ng ta fahimci cewa, Mista Kalu tsohon mamba na jam'iyyar PDP da ya rike kujerar gwamnatin jihar Abia a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, inda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a watan Nuwamba na shekarar 2016 da ta gabata.

KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Sama ta dauki Sabbin Dakaru 7, 000 cikin shekaru 3

Cikin martanin ta, jam'iyyar PDP ta bayyana cewa ko shakka ba bu Mista Orji ya bayyana ababen da suka shafe sa ne gami da iyawar sa da kuma yadda mai yiwuwa ya gudanar da al'amurransa.

A sanadiyar haka ne jam'iyyar ta PDP take kira ga tsohon gwamnan akan ya fito domin tantance su wa yake nufi da kalmar "mu" da ya yi amfani da ita cikin kalaman sa ya kuma bayyana yadda aka gudanar da kashe-kashen da ya yi ikirari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel