Tirkashi: 'Yan a ware na jam'iyyar APC a jihar Kaduna sun sake rabuwa gida biyu, sun fadi dalilinsu

Tirkashi: 'Yan a ware na jam'iyyar APC a jihar Kaduna sun sake rabuwa gida biyu, sun fadi dalilinsu

'Yan a ware na jam'iyyar APC a jihar Kaduna wanda akafi sani da 'APC Kaduna Restoration Group' sun sake rabuwa gida biyu. Tuni wadanda suka sake warewa sun zabi sabon ciyaman da sakatare da zai jagorance su.

Tun farko dai wasu ne da basu gamsu da irin salon mulkin Gwamna Nasir El-Rufai ba suka kafa tasu kungiyar karkashin jagorancin Tijjani Ramalan da kuma goyon baya daga Sanata Suleiman Hunkuyi wanda ake kyautata zaton yana goyon bayan tafiyar.

A wata taron manema labarai da suka kira a jiya Juma'a, sabon ciyaman na kungiyar, Awwal Fatoki ya ce sun yanke shawarar ballewa daga kungiyar Tijjani Ramalan ne saboda su mayar da kungiyar kan akidun da suka sanya aka kafa ta.

Tirkashi: 'Yan a ware na jam'iyyar APC a jihar Kaduna sun sake rabuwa gida biyu

Tirkashi: 'Yan a ware na jam'iyyar APC a jihar Kaduna sun sake rabuwa gida biyu

KU KARANTA: Matashi 'dan shekara 19 ya sayar da kaninsa kan kudi N20,000 don ya biya sadaki

Ya kuma ce sun fara gudanar da shirye-shirye na yin sulhu da uwar jami'iyyar APC na jihar Kaduna saboda su hada karfi waje daya su ciyar da jihar gaba.

Mista Fatoki ya koka kan yadda aka hadasa rashin jituwa tsakanin mutanen jihar Kaduna kuma ya ce dole a dakatar da wannan dabi'ar tare da cewa "Insha Allahu za mu hada karfi da karfe wajen ganin jam'iyyar APC ta yi nasara a babban zaben da ke zuwa a 2019."

A cewarsa kungiyar a ware din da aka kafa ta kauce daga ainihin akidun da aka kafa ta a kai.

"Shugabanin 'yan a ware din suna amfani da kungiyar ne kawai don cinma burinsu. Suna amfani da ita wajen tayar da fitina da kara raba kawunan al'ummar jihar Kaduna.

"Mun gano cewa ashe ana amfani da mu ne wajen yi wa jam'iyyar mu zagon kasa da kuma gwamnatin da ta kafa."

A bangarensa, wani jigo a kungiyar ta 'yan a ware, Hassan Mohammed ya ce wanda ke son barin kungiyar suna hakan ne kawai don biyan wasu bukatun kansu.

"Dama tun farko mun san ba su tare da mu. Mun san gwamnati su ke yi wa aiki. Suna son tayar da rikici ne amma hakan ba zai canja abinda kungiyar ta sa a gaba wajen aiwatar wa ba," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel