Yanzu-yanzu: Oyegun ya janye daga takaran kujeran shugaban jam'iyyar APC

Yanzu-yanzu: Oyegun ya janye daga takaran kujeran shugaban jam'iyyar APC

Shugaban jam'iyyar APC, John Odiegie-Oyegun, ya alanta ajiye niyyarsa na sake takaran kujeran shugabancin jam'iyyar APC a zaben da za'a gudanar ranan 23 ga watan Yuni, 2018

Oyegun ya bada wannan sanarwa ne yau Juma'a yayinda yake magana da manema labarai a Abuja.

Shugaban ya ce ba zai so ya zama matsala ko cikas ga jam'iyyar dubi ga irin rikice-rikicen da jam'iyyar ke ciki.

Yace: "Bani son in zama cikin matsala cikin jam'iyyar APC. Saboda haka ne ba zan sake takaran kujeran shugabancin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta kasa ba"

"Amma zan cigaba da aikina a matsayin shugaban jam'iyyar har lokacin da wa'adina ya kare ranan 25 ga watan Yni, 2018 yayinda za'a rantsar da sabbin shugabanni."

Zamu kawo muku cikakken rahoton....

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel