Idan na zama Gwamna zan kai Fayose gidan yari - Kayode Fayemi

Idan na zama Gwamna zan kai Fayose gidan yari - Kayode Fayemi

Babban ministan harkokin ma'adinai kuma daya daga cikin 'yan gaban goshin gwamnatin shugaba Buhari Mista Kayode Fayemi ya bayyana cewa jam'iyyar sa ta All Progressives Congress (APC) za ta tabbatar da cewa Gwamnan jihar Ekiti na yanzu ya je gidan yari da zarar ya sauka daga mulki.

Mista Fayeme kamar yadda muka samu yayi wannan ikirarin ne a lokacin da yake jawabi ga dumbin magoya bayan sa ranar Asabar din da ta gabata yayin taron gangamin sa na neman sake zama gwamnan jihar.

Idan na zama Gwamna zan kai Fayose gidan yari - Kayode Fayemi

Idan na zama Gwamna zan kai Fayose gidan yari - Kayode Fayemi

KU KARANTA: A Najeriya babu dan siyasar da bai sata - Gwamna Okorocha

Legit.ng dai ta samu cewa a wajen taron, Ministan na Buhari ya kara da cewa akwai ayyuka da dama da ya fara a jihar amma aka murde masa zabe aka hana shi ya karasa su shine ma dalilin da yasa ke son ya sake tsayawa takarar gwamnan jihar.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Ekiti dake zaman daya daga cikin manyan 'yan adawar shugaban kasa Muhammadu Buhari a Najeriya watau Gwamna Ayodele Fayose ya shawarci shugaban da ya janye kudurin sa na yin tazarce ya baiwa matasa dama masu jini a jika.

Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a dandalin sadarwar zamani na tuwita inda ya ce shekarun shugaban kasar sun wuce a ce yana mulkar 'yan Najeriya yanzu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel