Da dumin sa: Rundunar sojojin Najeriya ta rasa manyan kwamandojin ta 5 a jihar Borno

Da dumin sa: Rundunar sojojin Najeriya ta rasa manyan kwamandojin ta 5 a jihar Borno

Labarin da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa akalla jami'an rundunar sojojin Najeriya biyar ne suka rasa rayukan su sakamakon fashewar wasu nakiyoyi da 'yan ta'adda suka binne a jinar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya.

Kamar dau yadda muka samu, tuni har an kwashe gawarwakin wadanda suka rasa rayukan su zuwa asibitin rundunar sojojin ta bakwai dake a garin Maiduguri.

Da dumin sa: Rundunar sojojin Najeriya ta rasa manyan kwamandojin ta 5 a jihar Borno

Da dumin sa: Rundunar sojojin Najeriya ta rasa manyan kwamandojin ta 5 a jihar Borno

KU KARANTA: An jikkata Yarima Bin Salman a birnin Riyadth

Legit.ng ta samu sanarwar faruwar wannan lamarin ne a ta bakin mai magana da yawun rundunar sojojin Birgediya Janar Texas Chukwu wanda kuma yace lamarin ya auku ne a karamar hukumar Gwoza.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Buhari ta sha caccaka a wurin kungiyar shugabannin kiristoci ta kasar watau Christian Association of Nigeria (CAN) bisa zargin da suka yi na cewa an tambayi wadanda suka rubuta jarabawar daukar aikin 'yan sanda game da harshen larabci.

Ita dai kungiyar ta Christian Association of Nigeria (CAN) ta bayyana matsayar ta ne a cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun shugaban ta na kasa baki daya Rabaran Samson Ayokunle a ranar Alhamis din da ta gabata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel