Zaben 2019: Buhari sai ya riga rana faduwa inji wani Babban malamin addini

Zaben 2019: Buhari sai ya riga rana faduwa inji wani Babban malamin addini

Wani babban malamin addinin kirista a Najeriya mai suna Fasto Gabriel Adegboye ya yi hasashen cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai zarce ba a zaben da za'a yi na shekarar 2019.

Kamar yadda majiyar mu ta jaridar Nigerian tribune ta tuwaito, babban faston ya ayyana cewa ya samu wahayi ne daga ubangijin sa game da cewar wani sabon jini ne zai karbi mulki daga hannun shugaban kasar.

Zaben 2019: Buhari sai ya riga rana faduwa inji wani Babban malamin addini

Zaben 2019: Buhari sai ya riga rana faduwa inji wani Babban malamin addini

KU KARANTA: Hukumar NDLEA ta gano eka dubu 11 ta gonar wiwi

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Ekiti dake zaman daya daga cikin manyan 'yan adawar shugaban kasa Muhammadu Buhari a Najeriya watau Gwamna Ayodele Fayose ya shawarci shugaban da ya janye kudurin sa na yin tazarce ya baiwa matasa dama masu jini a jika.

Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a dandalin sadarwar zamani na tuwita inda ya ce shekarun shugaban kasar sun wuce a ce yana mulkar 'yan Najeriya yanzu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel