An damke babban malamin addini da laifin yin garkuwa da wani yaro

An damke babban malamin addini da laifin yin garkuwa da wani yaro

Jami'an 'yan sandan Najeriya sun sanar da samun nasarar cafke wani babban malamin addinin Kirista kuma Fasto a cocin Live By Faith dake a garin Ogbagu, na karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo mai suna Fasto Ifeanyi Nwachukwu bisa laifin satar dan shekara daya a duniya mai suna Damian Oluwa.

Haka ma dai tare da Faston, jami'an 'yan sandan sun kuma kama wani matashin mai shekaru 23 a duniya mai suna Miracle Emenekwuru duk dai da laifin na sata tare kuma da yin garkuwa da mutane.

An damke babban malamin addini da laifin yin garkuwa da wani yaro

An damke babban malamin addini da laifin yin garkuwa da wani yaro

KU KARANTA: Yaro dan shekara 14 ya zama Kwamishina a Bayelsa

Legit.ng ta samu cewa yan sandan sun ce da sun kammala cikakken bincike za su kai wadanda suke tuhumar a kotu.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa akalla jami'an rundunar sojojin Najeriya biyar ne suka rasa rayukan su sakamakon fashewar wasu nakiyoyi da 'yan ta'adda suka binne a jinar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya.

Kamar dau yadda muka samu, tuni har an kwashe gawarwakin wadanda suka rasa rayukan su zuwa asibitin rundunar sojojin ta bakwai dake a garin Maiduguri.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel