Dokar rage shekarun takara: Wani gwamna ya ce Buhari ya sauka, ya ba yara sabbin jini dama

Dokar rage shekarun takara: Wani gwamna ya ce Buhari ya sauka, ya ba yara sabbin jini dama

Gwamnan jihar Ekiti dake zaman daya daga cikin manyan 'yan adawar shugaban kasa Muhammadu Buhari a Najeriya watau Gwamna Ayodele Fayose ya shawarci shugaban da ya janye kudurin sa na yin tazarce ya baiwa matasa dama masu jini a jika.

Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a dandalin sadarwar zamani na tuwita inda ya ce shekarun shugaban kasar sun wuce a ce yana mulkar 'yan Najeriya yanzu.

Dokar rage shekarun takara: Wani gwamna ya ce Buhari ya sauka, ya ba yara sabbin jini dama

Dokar rage shekarun takara: Wani gwamna ya ce Buhari ya sauka, ya ba yara sabbin jini dama

KU KARANTA: Ba dan siyasa a Najeriya da bai sata - Gwamna Okorocha

Legit.ng dai ta samu cewa a jiya ne shugaban kasar ya sanya sabuwar dokar rage shekarun tsayawa takara a Najeriya hannu.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Buhari ta sha caccaka a wurin kungiyar shugabannin kiristoci ta kasar watau Christian Association of Nigeria (CAN) bisa zargin da suka yi na cewa an tambayi wadanda suka rubuta jarabawar daukar aikin 'yan sanda game da harshen larabci.

Ita dai kungiyar ta Christian Association of Nigeria (CAN) ta bayyana matsayar ta ne a cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun shugaban ta na kasa baki daya Rabaran Samson Ayokunle a ranar Alhamis din da ta gabata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel