Mutum 17m ne suka tsere daga Afirka a bara kadai - Majalisar dinkin barakar duniya

Mutum 17m ne suka tsere daga Afirka a bara kadai - Majalisar dinkin barakar duniya

- An sami yawan jama'a masu guduwa daga fatarar Afirka zuwa Turai

- Yawansu ya kai miliyan 17, daga Afirka a bara kawai

- Talauci, yake-yake, da rashin tabbas a rayuwa ke korar 'yan Afirka daga kasashensu

Mutum 17m ne suka tsere daga Afirka a bara kadai - Majalisar dinkin barakar duniya

Mutum 17m ne suka tsere daga Afirka a bara kadai - Majalisar dinkin barakar duniya

Rahoton motsin jama'a a duniya ya fito, inda ya nuna a bara kadai, 'yan Afirka miliyan 17 ne suka tsere daga Nahiyar ta Afirka zuwa yankunan da suka fi maiko a duniya.

Yawa-yawan wadanda suka tsere din, yunwa, yaki, fatara da talauci ke korarsu daga nasu kasashen, musamman ma rashin aikin yi wanda ke haifar da tabbas a rayuwa.

Jama'ar sun fi guduwa yankunan Turai ne domin neman na kai, da dora nauyinsu ga gwamnatoci masu karfi, wadanda suka san hakkin jama'a.

DUBA WANNAN: MTN zata fara biyan diyyar sace wa jama'a katin waya

Cikin rahoton kuma, ya nuna mutum miliyan biyar da rabi ne suka shiga Nahiyar daga sassan duniya, da niyyar zama ko aiki.

Wasu miliyan 19 kuma sun sauya matsugunansu a cikin dai Nahiyar ta Afirka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel