Wasu bankunan kasar nan na daf da rugujewa - Magu

Wasu bankunan kasar nan na daf da rugujewa - Magu

- Mista Magu ya bukaci bankuna da su bada jerin kwastomomi mara sa da'a kafin zuwan zaben 2019

- Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren tace matakin zai taimaka gurin yakar rashawa a kasar

Wasu bankunan kasar nan na daf da rugujewa - Magu

Wasu bankunan kasar nan na daf da rugujewa - Magu

Shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu, a ranar talata yace wasu daga cikin bankuna Najeriya sun kusa karyewa sakamakon aiyukan rashin dacewa na wasu mutanen.

A wata tataunawa tsakanin Magu da shugaban kungiyar kiyaye hakkin jami'an bankin Najeriya a ranar talata a jihar Legas, shugaban hukumar yaki da rashawan ya hori jami'an da su taimaka ta hanyar samar da bayanai ga hukumar.

DUBA WANNAN: MTN zata fara biyan diyyar sace wa jama'a katin waya

"Dole ne muyi kokarin ceto kasar nan. Da yawan bankunan nan sun kusa karyewa.

Nasan akwai tambayoyin da bazaku iya tambaya ba, ballantana in sun shafi wasu mutane, amma Idan kuka bamu bayanai akan mutanen, mu zamu iya. Idan akwai manyan matsalolin da zasu iya shafar bankunan ku, zaku iya bamu bayanai, balle yanzu da wani zaben ke gabatowa."

"Bana son in dinga tuhumar bankuna saboda wasu 'yan ta'adda saboda yin hakan zai iya kawo nakasa ga tattalin arzikinmu. Zai iya hana masu sa hannayen jari zuwa kasar. "

"Kowane banki na iya samun matsala, komai shaharar shi. Shiyasa muke so muga baku fada matsala ba. A shirye muke don hada kai daku don ganin cigaban tattalin arzikin kasar nan. A shirye muke don ganin mun karbo muku basussukan da kuke bi amma fa in kun dage da aiyukan ku."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel