Dalilin da yasa na zauna a bangaren 'yan jam'iyyar PDP - Dino Melaye

Dalilin da yasa na zauna a bangaren 'yan jam'iyyar PDP - Dino Melaye

Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma Sanata Dino Melaye ya yi bayanin dalilin da yasa ya kozauna a bangaren da 'yan majalisar jam'iyyar PDP ke zaune a majalisar dattawan bayan dawowansa majalisar.

Sanatan dai ya nemi a taimaka masa ya zauna a bangaren da sanatocin jam'iyyar adawa ta PDP ke zama ne a ranar Laraba da ta gabata.

Dino Melaye ya yi ikirarin cewa ya hangi zaki da damisa da macizai ne a kujerarsa na da hakan yasa ya nemi a canja masa wajen zama kamar yadda ya rubuta a shafinsa na dandalin sada zumunta na Instagram.

Dalilin da yasa na koma bangaren 'yan jam'iyyar PDP - Dino Melaye

Dalilin da yasa na koma bangaren 'yan jam'iyyar PDP - Dino Melaye

"Na ga zaki da damisa da macizai a wannan kujerar. Ku canja min wajen zama," kamar yadda Sanatan ya rubuta a shafinsa na Instagram.

KU KARANTA: Asiri ya sake tonuwa: Wata daliba ta sake tona asirin wani Farfesa da ke neman kwanciya da ita

Sanatan ya kwashe makoni yana asibiti inda ya ke karbar magunguna sakamakon raunukan da ya samu a yayinda ya daka tsalle daga cikin motar yan sanda a hanyar su na tafiya da shi kotu don ya amsa tambayoyi a kan tuhumar da ake masa na daukan nauyin yan baranda.

Bayan isar sa majalisar Sanata Dino Melaye wanda ke sanye da abinda ke tallafa masa wajen tsayar da wuyansa, ya yi kira ga shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki da ya sama masa kujera a bangaren mambobin majalisar da ke karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Hakan dai ya jawo cece-kuce a majalisar sakamakon zargin da wasu mambobin majalisar ke yi na cewa zai Sauya Sheka zuwa jam’iyyar PDP sai dai shi Sanata Dino Melaye bai bayyana cewa ya koma jam’iyyar ta PDP ko akasin hakan ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel