An kashe yan Najeriya guda 3 a kasar Indiya an tsinci gawarakinsu a dakinsu

An kashe yan Najeriya guda 3 a kasar Indiya an tsinci gawarakinsu a dakinsu

An tsinci gawarwakin wasu yan Najeriya guda uku dake karatu a kasar Indiya a dakinsu dake yankin Uttam Nagar Mohan, a babban birnin Delhi, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da sanyin safiyar ranar Juma’a, 1 ga watan Yuni ne wasu makwabtan yan Najeriya suka gano gawarwakin daliban, inda ba tare da wata wata ba suka kai rahoto zuwa ofishin Yansandan yankin.

KU KARANTA: An ci an sha yayin da Buhari ya karbi bakoncin Dangote da hamshakan yan kasuwa a Villa

Rahotanni sun tabbatar da cewar ba tare da bata lokaci jami’an Yansanda suka mamaye gidan, daga bisan suka gayyato wasu kwararrun masu binciken kwakwaf da zasu taimaka wajen zakulo wadanda suka kashe daliban.

An kashe yan Najeriya guda 3 a kasar Indiya an tsinci gawarakinsu a dakinsu

Kasar Indiya

Su dai wadannan kwararru da ake kiransu da suna ‘Forensic Expert’ a Turance suna amfani ne da sawun kafa, sawun hannu, da sauran abubuwan da zasu iya gani a cikin dakin wajen gano masu hannu cikin kisan yan Najeriya.

Sai dai zuw yanzu babu wani tabbataccen dalilin mutuwar tasu, amma dai Yansanda sun tabbatar da cewar babu wata alamar ciwo a jikkunansu duka su ukun.

Tun a shekarar data gabata ne ake yawan samun mutuwar yan Najeriya a kasar Indiya, kodai yan kasar zauna gari banza su kashe su, ko dai Yansanda su kashe su, ko kuma yan Najeriya abokan gaba su kashe kawunansu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel