Aika ji irinta: Wani Saurayi ya yiwa Budurwar da suka hadu ta Facebook Fyade

Aika ji irinta: Wani Saurayi ya yiwa Budurwar da suka hadu ta Facebook Fyade

- Wani Matashi yayi baranbarama ga budurwarsa da suka hadu ta kafar sada Zumunta

- Sai dai asirinsa ya tonu har ma ya fada komar 'Yan sanda

- Yanzu haka idonsa ya fara raina fata a gaban Kotu

Wani alkalin Kotun majistire dake zamanta a Ikeja a jihar Legas ya bada umarnin tsare wani matashin dan kasuwa mai suna Ebuka Eze bisa tuhumarsa da aikata da laifin yiwa wata Yarinya mai shekaru 16 fyade wadda suka hadu a kafar sada zumunta ta facebook.

Aika ji irinta: Wani Saurayi ya yiwa Budurwar da suka hadu ta Facebook Fyade

Aika ji irinta: Wani Saurayi ya yiwa Budurwar da suka hadu ta Facebook Fyade

Bayan tattara bayanai da alkalin kotun P. E Nwaka ya yi, ya bada umarnin a tsare matashin mai shekaru 27 a gidan kaso na kirikiri dake jihar ta Legas har zuwa zaman Kotun na gaba.

Matashin da ake tuhuma yana zaune ne a gida mai lamba 25 Mafoluku dake unguwar Oshodi ta jihar Legas inda ya yi kokarin aikata laifin fyaden ga Yarinyar.

KU KARANTA: ‘Yan sanda sun shiga cakwakiya, zasu biya har Naira Miliyan 10, ko mai yayi zafi?

Mai shigar da kara a gaban kotu ya bayyanawa alkalin cewa matashin ya aikata wannan laifi ne a gidansa tun a ranar 19 ga watan Mayun 2018. Mai shigar da kara ya cigaba da cewa sun hadu da yarinyar ne a kafar sada zumunta ta facebook inda daga bisani ya bukaci ta kawo masa ziyara wanda hakan ya bashi damar yi mata haike mata.

Aika ji irinta: Wani Saurayi ya yiwa Budurwar da suka hadu ta Facebook Fyade

Aika ji irinta: Wani Saurayi ya yiwa Budurwar da suka hadu ta Facebook Fyade

Mai shigar da karar ya ce "Ya gayyace ta zuwa gidansa bayan isowar ta sai ya tura ta kan gado inda ya rufe mata baki da filo sannan ya aikata wannan ta'asa, amma daga bisani sai ya cire tare da goge zanin gadon wanda ya baci da jinin jikin yarinyar."

"Bayan yarinyar ta isa gida sai iyayenta suka lura da jini a jikinta, wanda suka tuhume ta game da abinda ya faru ta kwashe labari ta fada musu."

"Iyayen basu bata lokaci ba suka kai kara ofishin hukumar ‘Yan sanda, wanda nan take aka je aka kamo wannan matashi."

Wannan laifi da matashin ya aikata dai ya sabawa sashi na 260, na kudin manyan laifuka na jihar Legas na shekara ta 2015.

Yanzu haka dai kotun ta dage zaman nata har sai zuwa 28 ga watan Yuni 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel