Mutane 17m sun haure daga Nahiyyar Afirka domin Tafiya Cirani - UN

Mutane 17m sun haure daga Nahiyyar Afirka domin Tafiya Cirani - UN

Mun samun rahoton cewa Majalisar 'Dinkin Duniya ta bayyana adadin al'ummar Afirka da suka yi ƙaura domin fita cirani zuwa wasu kasashen dake wajen nahiyyar ta Afirka.

Majalisar ta bayyana cewa kimanin mutane Afirka Miliyan 17 ne suka yi ƙaura domin fita cirani daga nahiyyar zuwa wasu nahiyoyin na duniya.

A yayin taron masana'antu da ci gaba da aka gudanar, majalisar ta bayyana sakamakon kididdigar bakin haure dake kasashen duniya daban-daban, inda ta bayyana cewa kimanin mutane Miliyan 5.5 ne suka hauro zuwa nahiyyar Afirka.

'Yan Afirka 17m sun haure domin Tafiya Cirani a 2017

'Yan Afirka 17m sun haure domin Tafiya Cirani a 2017

Binciken majlisar ya kuma bayyana yadda kimanin Mutane Miliyan 19 na bakin haure daga wasu nahiyoyin suka taho cirani zuwa nahiyyar Afirka.

KARANTA KUMA: Sufeton 'Yan sanda ya bayyana dalilin rashin amsa gayyatar Majalisar Dattawa

Wani Babban Sakatare na Majalisar, Mukhisa Kituyi, shine ya bayyana hakan yayin taron kasuwanci da aka gudanar, inda ya bayyana cewa binciken ya tabbatar da wannan adadi na Miliyoyin Al'umma da 'iyalan su dake cirani a nahiyyar Afirka.

Jagoran wallafa wannan sakamako, Junior Davis, ya bayyana cewa wannan bincike ta tabbatar da babbar alakar dake tsakanin bakin haure da kasuwanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel