Rikicin APC: Dogara zai jagoranci ‘Yan nPDP su gana da Uwar Jam’iyya

Rikicin APC: Dogara zai jagoranci ‘Yan nPDP su gana da Uwar Jam’iyya

Daily Trust ta rahoto cewa an shirya wani kwamiti na mutunae 9 da za ta zauna domin dinke barakar da ake samu tsakanin tsofaffin ‘Yan Jam’iyyar PDP da ke cikin APC da Uwar Jam’iyyar. Tun kwanaki ‘Yan nPDP su ka aikawa Shugaba Buhari takarda.

Rikicin APC: Dogara zai jagoranci ‘Yan nPDP su gana da Uwar Jam’iyya

Yakubu Dogara da sauran 'Yan nPDP za su zauna da APC

A Ranar Litinin mai zuwa ne za a cigaba da zama domin shawo kan karshen banbancin da aka samu tsakanin ‘Yan nPDP da APC. ‘Yan nPDP sun nada Shugaban Majalisar Wakilai Rt. Hon. Yakubu Dogara ya jagorance su wajen zaman da za a fara yi a Ranar Litinin.

Kwamitin da aka shirya ya gana da Uwar Jam’iyyar ya kunshi wasu mutum 4 daga Fadar Shugaban Kasa da APC da kuma mutane 5 daga ‘Yan nPDP. Yanzu dai har an aikawa Shugaban Kasa Buhari sunayen wadanda za a zauna din da su kamar yadda mu ke ji.

KU KARANTA: Wani sabon rikici na nema ya barke a Jam’iyyar APC a Oyo

Yan nPDP dai sun hada da Shugabannin Majalisar Tarayya da wasu Sanatocin da ‘Yan Majalisu da tsofaffin Gwamnoni da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal. Abubakar Kawu Baraje shi ne Shugaban ‘Yan nPDP kuma yana cikin wadanda kwamitin da aka kafa.

Sauran ‘Yan nPDP da za su gana da manyan da ke Fadar Shugaban Kasar su ne Sanata Danjuma Goje. Bernabas Gemade, da kuma Adamu Aliero. Bukola Saraki da irin su Sanata Kwankwaso ba su cikin wadanda za su zauna da Uwar Jam’iyyar a makon gobe.

Tun tuni dai kun ji cewa Jagororin na nPDP sun koka ne game da yadda aka yi zaben shugabannin Jam’iyyar a Jihohi. Yanzu dai za ayi kokarin dinke duk barakar da aka samu tsakanin tsofaffin ‘Yan PDP da Uwar Jam’iyyar inji Shugaban APC Lawan Shuaibu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel