Manyan APC a Jihar Oyo sun kai karar na-hannun daman Gwamna wajen Buhari

Manyan APC a Jihar Oyo sun kai karar na-hannun daman Gwamna wajen Buhari

- Manyan Jam’iyyar APC a Jihar Oyo sun kai kuka wajen Shugaba Buhari

- ‘Ya ‘yan Jam’iyyar sun koka game da yadda aka gudanar da zaben Jihar

- Na-kusa da Gwamna ba su biya kudin takara ba amma su ka nemi kujera

Dazu ne mu ka ji cewa wasu manyan Jam’iyyar APC sun koka da abin da ya faru wajen zaben shugabannin Jam’iyyar da aka yi kwanaki a Jihar Oyo. Yanzu ta kai sun kai kuka wajen Shugaban kasa.

Manyan APC a Jihar Oyo sun kai karar na-hannun daman Gwamna wajen Buhari

Wasu 'Yan APC a Jihar Oyo su na rikicin shugabanci
Source: Depositphotos

A Jihohi da dama dai an koka game da yadda aka gudanar da zaben Jihohi kwanaki inda wasu a APC su ke ganin abin da ya faru na iya jefa Jam’iyyar cikin matsala a 2019. Wasu ‘Ya ‘yan Jam’iyyar ne karkashin tafiyar Unity Forum su ke korafi.

KU KARANTA:

Legit.ng ta ji cewa ana zargin na-kusa da Gwamnan Jihar Oyo Abiola Ajimobi da tsayawa takara duk da ba su saye fom din takarar ba. Dalilin haka ne wasu daga cikin ‘Yan Jam’iyyar mai mulki su ka kai kuka wajen Shugaban kasa da uwar Jam’iyya.

Har dai ta kai Sakataren ‘Yan Kungiyar “Unity Forum” a Jam’iyyar watau Wasiu Olatunbosun yace wadanda ke tare da Gwamna Ajimobi na barazana ga rayuwar su. Don haka ne dai su ka nemi Shugaba Buhari ya sa baki a wannan rigimar ta su tun wuri.

Dazu kun ji labari cewa Gwamnan Jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi wanda shi ne shugaban kwamitin sadarwa na shirin zaben APC na-kasa gaba daya da za ayi kwanan nan ya bayyana cewa ana kokarin dinke barakar da ke Jam’iyyar APC mai mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel