Majalisar Tarayya ta kawo wasu sauye-sauye a zabe mai zuwa

Majalisar Tarayya ta kawo wasu sauye-sauye a zabe mai zuwa

Mun samu labari daga manema labarai na Kasar nan cewa a makon nan ne Majalisar Wakilai ta Tarayyar Najeriya tace sam ba ta yarda ayi amfani da na’urar zamani a wajen ainihin kada kuri’a a zabe mai zuwa na 2019 ba.

Majalisar Tarayya ta kawo wasu sauye-sauye a zabe mai zuwa

Majalisar Najeriya tace ba za ayi amfani da na'ura wajen kada kuri'a ba

‘Yan Majalisar Tarayyar sun yi watsi da kokarin da ake yi na yi wa tsarin zabe garambawul. Sai dai kuma Majalisar ta amince ayi amfani da katin nan na zamani watau “Smart Card” wajen tantance masu shirin kada kuri’a.

Wani ‘Dan Majalisa ne ya kawo wani kudiri da zai kawo gyara a harkar zabe, sai dai ‘Yan Majalisar ba su yi na’am da duk abin da kudirin ya kunsa ba. Kudirin na kokarin ganin an koma dangwala kuri’ar ne da na’uran zamani.

KU KARANTA: Don kun dawo APC bai hana a kama ku - Buhari

Yanzu dai babu maganar dangwala kuri’a da na’ura mai kwakwalwa bayan da Majalisar tace za a cigaba da kada kuri’ar ne kamar yadda aka saba ke-ke-da-ke-ke da hannu. Za ayi amfani da na’ura ne kurum wajen tantance mai zabe.

Da zarar dai an samu matsala da na’urar wajen tantance ma su shirin kada kuri’a za a dakatar da zaben wurin. Haka kuma kudirin ya yarda aci tarar wanda aka samu ya tsaya takara da takardun bogi a kuma hana shi sake fitowa zabe.

Kun san cewa wannan karo dai an yi amfani ne da na’ura mai kwakwalwa wajen zaben Kananan Hukumomin Jihar Kaduna. Majalisar Tarayya dai ba ta yarda ayi amfani da na’ura wajen kada kuri’a a zaben kasar da za ayi a 2019 ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

‘Yan Majalisar Najeriya ba su yarda a sauya tsarin zabe a 2019 ba

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel