Shugaba Buhari da Saraki sun mika ta'aziyarsu kan rasuwar shugaban wata jaridar Najeriya

Shugaba Buhari da Saraki sun mika ta'aziyarsu kan rasuwar shugaban wata jaridar Najeriya

Allah ya yi wa Ciyaman din Punch Nigeria Limited, Mr. Gbadebowale Wayne Aboderin rasuwa. Marigayin mai shekaru 60 a duniya ya rasu ne a jiya Laraba 30 ga watan Mayun 2018 bayan anyi masa tiyata a zuciya a asbitin First Cardiology Consultants da ke Legas.

Aboderin ya maye gurbin Cif Ajibola Ogunsola ne a matsayin ciyaman din Punch a ranar 1 ga watan Mayun 2011 bayan Ogunsola ya yi murabus a ranar 30 ga watan Afrilun 2011 inda ya kwashe shekaru 24 a matayin shugaban jaridar.

Kafin nadinsa a matsayin ciyaman din jardiar, Aboderin wanda dan kasuwa ne kuma da ga wanda ya kafa jaridar Punch, marigayi Cif Olu Aboderin, an nada shi mamba na kwamitin direktocin kamfanin a ranar 21 ga watan Yulin 1984 kuma ya zama mataimakin Ciyaman din kamfanin a ranar 2 ga watan Yuni na 2010.

Shugaba Buhari da Saraki sun mika ta'aziyarsu kan rasuwar shugaban wata jaridar Najeriya

Shugaba Buhari da Saraki sun mika ta'aziyarsu kan rasuwar shugaban wata jaridar Najeriya

An haifi marigayin ne a ranar 17 ga watan Afrilun 1958 a birnin Landan da ke kasar Ingila kuma ya yi karatu har ya zama kwararen matukin jirgin sama kuma ya kasance mai sha'awan wasan kwallon kwando ne.

KU KARANTA: Fusatattun matasa sun bankawa motar jami'an kwastam wuta, kalli hotuna

Marigayin ya rasu ya bar matan aure daya Titilayo da yara.

A sakon ta'aziyarsa wanda ta fito ta hannun hadiminsa na fanin yadda labarai Garba Shehu, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana marigayin a matsayin dan kasuwa da ake mutuntawa kuma mai taimakon al'umma wanda ya bayar ga gagarumin gudunmawa a aikin jarida.

A bangarensa, Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana marigayin a matsayin mai taimakon talakawa, mai sha'awan wasanin motsa jiki kuma dan kasuwa da ya bar abubuwan alheri da ba za'a taba mantawa da shi ba.

Yakubu Dogara da Atiku Abubakar da Bola Tinubu da Gwamna Samuel Ortom da Gwamna Ayodele Fayose duk sun mika ta'aziyarsu ga iyalansa da daukakin abokan aikinsa tare da yin addua'a Allah ya gafarta masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel