Not Too Young To Run: PDP ta yabawa wadanda su ka jajirce Matasa su ka samu galihu

Not Too Young To Run: PDP ta yabawa wadanda su ka jajirce Matasa su ka samu galihu

- PDP ta yi murna da Shugaba Buhari ya sa hannu kan kudirin “Not Too Young To Run”

- Jam’iyyar ta yabawa wadanda su ka yi bakin kokarin wajen kai ga wannan nasara jiya

-PDP tace Buhari ya daina jin shi yayi aikin don kuwa Majalisa ce ta gama masa komai

Mun samu labari cewa babban Jam’iyyar adawa a Najeriya watau PDP ta yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na sa hannu da yayi kan kudirin nan na ‘Not Too Young to Run’ a jiya. PDP tace a 2019 kuma za ta tafi da Matasa.

Not Too Young To Run: PDP ta yabawa wadanda su ka jajirce Matasa su ka samu galihu

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kudirin Not Too Young To Run
Source: Depositphotos

A jiya da rana ne Shugaban Kasar ya rattaba hannun sa a kan wannan kudiri da ya zama doka a Fadar Shugaban Kasa. Hakan dai zai bada dama Matasa har ‘Yan shekara 25 su tsaya takarar kujerar Majalisar Tarayya a Najeriya.

KU KARANTA:

Sakataren yada labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa watau Kola Ologbondiyan ya yabawa Shugaban Kasa Buhari da ya sa hannun-sa inda ya kira wannan mataki da aka dauka a matsayin nasara ga Matasan Kasar nan baki daya.

Kola Ologbondiyan ya kuma yabawa kokarin Honarabul Tony Nwulu wanda ya fara kawo kudirin gaban Majalisa. Haka kuma Jam’iyyar dai ta kuma yi kira ga Matasa da su yi amfani da wannan damar da aka samu a Najeriya.

Jam’iyyar ta kuma jinjinawa Matasan da su ka dauki wannan abu a ka har aka dace ya zama doka. Sai dai PDP tace Jam’iyyar APC ba ta taka rawar gani wajen ganin wannan kudiri ya samu shiga ba saboda ‘Dan PDP ya kawo maganar.

Ologbondiyan ya bayyana cewa ka da Shugaba Buhari ko APC su rika jin cewa su ne su kayi ruwa-da-tsaki wajen aikin wannan kudiri. Ologbondiyan yace Shugaban Kasar ya rattaba hannun sa ne bayan an kammala komai a Majalisa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel