Ana nan ana kokarin yin sulhu tsakanin ‘Ya ‘Yan Jam’iyyar APC - Ajimobi

Ana nan ana kokarin yin sulhu tsakanin ‘Ya ‘Yan Jam’iyyar APC - Ajimobi

Mun samu labari dazu cewa kawo yanzu dai kwamitin da ke shirin zaben shugabannin Jam’iyyar APC na kasa na cigaba da sulhunta ‘Yan Jam’iyyar. Har yanzu akwai rigimar cikin-gidan a APC.

Gwamnan Jihar Oyo Abiola Ajimobi wanda shi ne shugaban kwamitin sadarwa na shirin zaben APC na-kasa gaba daya da za ayi ya bayyana ana kokarin dinke barakar da ke APC kuma an bar kujerun da za ayi takara ga duk mai niyya.

Ana nan ana kokarin yin sulhu tsakanin ‘Ya ‘Yan Jam’iyyar APC - Ajimobi

APC za ta ba kowa dama yayi takara a zaben kwanan nan

Abiola Ajimobi ya bayyana cewa duk da Shugaban Kasa Buhari yana bayan Adams Oshiomole, sai dai hakan bai hana duk wanda yake sha’awar zama shugaban Jam’iyyar ya fito takara ba domin kuwa tsari ne na Damukaradiyya.

KU KARANTA: Sheikh Gumi yayi tir da abin da aka yi wa tsohon Gwamnan PDP

Gwamnan na APC ya bayyana wannan ne lokacin da yake magana da ‘Yan Jarida inda ya kuma bayyana cewa kwamitin Bola Tinubu da aka nada domin dinke barakar da ke cikin Jam’iyyar na nan tana cigaba da aikin ta a boye.

A dalilin sulhun da ake yi a Jam’iyyar ne ma dai aka samu wasu da su ka fusata a da, su ka shigar da Jam’iyyar kara a Kotu sun janye karar a yanzu. Ajimobi ya kuma nuna cewa rikicin da aka samu wajen zaben Jihohi ba wani abu bane.

Dama dazu kun ji cewa tsohon Mataimakin Gwamnan babban bankin Najeriya Kingsley Moghalu zai fito takarar Shugaban Kasa a 2019 karkashin YPN. Shugaban Kasa Buhari mai shekara 74 a Duniya yana sa ran zarcewa a kan karagar mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel