‘Yan sanda sun shiga cakwakiya, zasu biya har Naira Miliyan 10, ko mai yayi zafi?

‘Yan sanda sun shiga cakwakiya, zasu biya har Naira Miliyan 10, ko mai yayi zafi?

- Duniya juyi-juyi inji masu iya magana

- 'Yan sanda sun ga ta kansu a gaban wani alkali bayanda suka bindige wani Mutum har Lahira

- Da alama dai hukunci da ake yanke ba zai musu dadi ba

Wata babbar kotu dake zamanta a garin Ibadan ta bawa hukumar 'Yan sanda ta Jihar umarnin biyan diyyar kudi har Naira Miliyan N10m ga iyalan direban da Jami'in 'Yan sandar jihar ya kashe akan Saki-Okere.

‘Yan sanda sun shiga cakwakiya, zasu biya har Naira Miliyan 10, ko mai yayi zafi?

‘Yan sanda sun shiga cakwakiya, zasu biya har Naira Miliyan 10, ko mai yayi zafi?

Jami'in Dan sandan mai suna Ifenyi Onynbu mai mukamin Sufeto ya yi sanadiyyar mutuwar Hakeem har Lahira ta hanyar harbi da bindigar da yayi masa a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2016 a daidai kan Titin kasuwar Saki-Okere.

‘Yan sanda sun shiga cakwakiya, zasu biya har Naira Miliyan 10, ko mai yayi zafi?

‘Yan sanda sun shiga cakwakiya, zasu biya har Naira Miliyan 10, ko mai yayi zafi?
Source: UGC

Bayan rasuwar direban motar, Dansa ya yi amfani da hukumar kare hakkin Dan Adam wajen shigar da kara a kotu domin kalubalantar rundunar yan sandan ta jihar.

Mutanen da ake karar sun hada da shugaban rundunar yan sanda na kasa, shugaban rundunar ‘Yan sanda na jihar sai kuma shugaban ‘Yan sanda na yankin Saki inda abin ya faru.

Mai shigar da karar tun fari sun bukaci kotun da ta nema musu Miliyan dari biyar 500 a matsayin diyya. Mai karar ya bayyanawa kotun cewar Dan sandan ya kashe mahaifinsa ne domin ya ki bashi cin-hancin naira 100, wanda hakan har ya jawo ya harbe shi a kai.

KU KARANTA: Tsugunni bata kare ba: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane 25 a jihar Kaduna

Sai dai Alkalin kotun mai suna Nathaniel Ayo-Emmanuel ya ce kowane dan kasa yana da iko da damar yin rayuwa cikin sukuni ba tare da tsangwama ba balle har ta kai ga kisa, ya ce tabbas kashe mamacin ya sabawa dokar shari'a.

Bayan saurara bayanai daga bakin shaidu alkalin kotun ya yi nazari tare da bayyanawa cewa Kwamishinan yan sanda na jihar oyo da kuma shugaban yan sanda na shelkwatar Saki dukkansu suna da laifi kuma alkalin ya bukaci da su biya iyalan mamacin diyya har ta naira miliyan 10

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel