Sheikh Gumi ya ɓara kan yadda EFCC ta wulakanta Tsohon gwamnan jihar Kaduna

Sheikh Gumi ya ɓara kan yadda EFCC ta wulakanta Tsohon gwamnan jihar Kaduna

Sanannen Malamin addinin Islama dake jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi ya bayyana bacin ransa gami da damuwa game da yadda hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta wulakanta tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Malamin ya bara ne a yayin gabatar da tafsirin Al-Qur’ani kamar yadda ya saba yi a watan Ramadan, inda yace EFCC ba ta da hurumin bayyana mutum a matsayin mai laifi, don haka bai kamata su yi ma Ramalan abinda suka yi masa ba.

KU KARANTA: An ci an sha yayin da Buhari ya karbi bakoncin Dangote da hamshakan yan kasuwa a Villa

A cikin bayanin Malamin ya bayyana cewa yaso ace Ramalan bai baiwa EFCC hadin kai ba, “Dama an dauke shi ne yana fada dasu akan bai yarda ba, wannan shi yafi.” Inji Malamin.

Gumi bai karkare jawabinsa ba har sai da ya bayyana bacin ransa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda da ana bin laifi da Buhari bai zama shugaban kasa ba.

“Mutanen Kudu sun yi hannu riga da gwamnatin nan, Mutanen Arewa ne kawai suke binsa, dakikan mutane, a auna Buhari da tsohon shugaban kasa Shagari a gani wanene ya ci kudin gwamnati?” Inji Dakta Gumi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel