Fusatattun matasa sun bankawa motar jami'an kwastam wuta, kalli hotuna

Fusatattun matasa sun bankawa motar jami'an kwastam wuta, kalli hotuna

Wasu fusatattun matasa a unguwar Oron da ke jihar Akwa Ibom sunyi arangama da jami'an hukumar yaki da masu fasakwabri na kasa wanda akafi sani da Kwatsam a mahadar hanyar Uya-Oro.

Rikicin ya barke ne yayinda jami'an kwastam din suka harbi tayar wata babban mota dauke da shinkafa wadda aka shigo da ita ta barauniyar hanya kuma suke kokarin tserewa ta unguwar na Oro.

Harbin tayar motan ya sanya motar ta kubcewa direban babban motan har ya kai ga fadawa wani dan achaba da ke dauke da yara 'yan makaranta da fasinjoji biyu kuma ya yi musu mumunan rauni.

Fusatattun matasa sun bankawa motar jami'an kwastam wuta, kalli hotuna

Fusatattun matasa sun bankawa motar jami'an kwastam wuta, kalli hotuna

KU KARANTA: 2019: Zan azurta ku da miliyoyi idan ku ka sake zabe na - Gwamnan wata jihar Arewa

Wani wanda abin ya faru a idanunsa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce daya daga cikin fasinjojin da dan achaban ya dauko ya rasu nan take.

Fusatattun matasa sun bankawa motar jami'an kwastam wuta, kalli hotuna

Fusatattun matasa sun bankawa motar jami'an kwastam wuta, kalli hotuna

Ya ce abin ya faru misalin karfe 3 na yammacin jiya.

Hakan yasa matasan unguwar suka fadawa jami'an kwastam din da duka kana daga baya suka bankawa motar wuta.

Yayin da ya ke tsokaci a kan lamarin, Kakakin hukumar yan sanda na jihar, DSP MacDon Achebe ya tabbatar da afkuwar lamarin.

"Jami'an kwastam din sun harbi tayar wata mota da ke kokarin tserewa, hakan yasa motar da fadawa dan achaba dauke da fasinjoji," inji Achebe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel