Yaki da ta’addanci: Sojojin Najeriya sun ceto mutane 9 sun halaka mayakan Boko Haram 3

Yaki da ta’addanci: Sojojin Najeriya sun ceto mutane 9 sun halaka mayakan Boko Haram 3

Dakarun rundunar Sojan kasa sun samu nasarar ceto mutane tara daga hannun mayakan Boko Haram tare da halaka yan ta’adda guda uku a yayin aikin kakkabe sauran yan ta’adda da suka rage a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar Sojin kasa, Birgediya Texas Chukwu ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, 31 ga watan Mayu, inda yace Sojoji a yayin wata samame da suka kai kauyukan Jaje, Angwar Audu, Major Ali, Dabu Abdullahi, Dabu Wulkaro da Gori Jaji sun ceto mutane 9 da yan ta’adda suka yi garkuwa dasu.

KU KARANTA: Tsugunni bata kare ba: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane 25 a jihar Kaduna

Daga cikin wadanda Sojojin suka kwato akwai Maza tsofaffi guda biyu, mata biyu, da kuma kananan yara guda biyar, inda a yanzu haka rundunara ta garzaya dasu zuwa Asibiti don duba lafiyarsu.

Yaki da ta’addanci: Sojojin Najeriya sun ceto mutane 9 sun halaka mayakan Boko Haram 3

Yaki da ta’addanci: Sojojin Najeriya

Kaakakin ya kara da cewa a yayin karanbattan, Sojoji sun samu nasarar karkashe yan ta’adda guda uku, baya da haka sun gano buhunan abinci da yan ta’addan suka binne, tare da dabbobi da dama da suka sata.

Daga karshe sanarwar ta bukaci jama’a da su cigaba da kai rahoton duk wani ko wata da basu gane take takensu ba ga hukumomin tsaro don magance faruwar abinda ba a so.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel