Tsugunni bata kare ba: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane 25 a jihar Kaduna

Tsugunni bata kare ba: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane 25 a jihar Kaduna

Wasu gungun yan bindiga dauke da muggan makamai sun far ma babbar hanyar da ta hada Birnin Gwari na jihar Kaduna zuwa Funtua na jihar Katsina, inda suka sace fiye da mutane 25, inji rahoton jaridar The Cables.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun dira a kauyen Kiryoyi da Maganda, inda suka dinga tare motoci, suna tasa keyar fasinjojin motocin zuwa wani daji, kamar yadda shugaban kungiyar NURTW ya bayyana.

KU KARANTA: Idanun wani Lebura da ya casa Dansanda sun raina fata bayan da Kotu ta yanke masa hukunci

Shugaban kungiyar NURTW reshen karamar hukumar Birnin Gwari, Danladi Duniya yace: “Bani da hurumin tabbatar muku da adadin mutanen da aka sace, amma fa suna da yawa, don zasu kai mutum 25 ko ma fiye da haka, amma fa sun sace dukkanin Fasinjojin motocin da suka tare.

Tsugunni bata kare ba: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane 25 a jihar Kaduna

Titin Birnin Gwari

“Motoci 5 suka tare, amma wani direban dake tuka wata motar Golf ya samu nasarar tserewa, wannan itace matsalar da muke fama da ita a hanyar nan a kullum, don haka muke kira ga gwamnati da ta kawo mana agaji, bama iya zuwa gona, bama iya kai ziyara.” Inji shi.

A wani labarin kuma, a satin data gabata ne yan bindiga suka cika hannu da mutane 44 a karamar hukumar Birnin Gwari dake cikin wasu ayarin motoci guda biyar, inda yan bindigan suka yi garkuwa dasu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel