An dakatar da ni a Majalisa yayin da na faɗi irin abin da Jega ya faɗa - Yerima

An dakatar da ni a Majalisa yayin da na faɗi irin abin da Jega ya faɗa - Yerima

Wani tsohon dan Majlisar Wakilai, Dakta Haruna Yerima, ya bayyana hukuncin da aka majalisar ta zartar a kansa yayin da ya furta makamancin kulamin tsohon shugaban hukumar zabe, Farfesa Attahiru Jega.

A makon da ya gabata ne tsohon shugaban hukumar zabe ya bayyana cewa ko shakka ba bu cin hanci da rashawa ya mamaye majalisar dokoki ta tarayya.

Dakta Haruna ya bayyana cewa, makamancin wannan furuci na Farfesa Jega shi ya sanya aka dakatar da shi daga majalisar shekaru 13 da suka gabata.

Farfesa Attahiru Jega

Farfesa Attahiru Jega

A yayin ganawa da maname labarai na jaridar Daily Trust a ranar Alhamis din da ta gabata, Yerima ya goyi bayan Jega dangane da wannan gaskiya da ya furta inda yake cewa majalisar ba ta hujja ko guda da za ta kare kanta dangane da annobar rashawa da ta mamaye ta.

Tsohon dan majalisar ya bayyana cewa, rashawa tayi kaka-gida cikin kwamitocin da aka wakilta wajen sanya idanun lura akan wasu cibiyoyi da ma'aikatun gwamnatin tarayya.

KARANTA KUMA: Ana Fafutikar Ceto 'Yan Matan Chibok da 'Dalibar Dapchi ta 'Karshe - Hukumar Sojin Kasa

Hakazalika tsohon shugaban hukumar zabe ya bayyana cewa, mambobin majalisar dokoki ta tarayya sun damalmala hannayen su cikin kazantar rashawa da wasu ma'aikatun gwamnati domin aikata magudi cikin kasafin kudi.

A yayin mayar da martani dangane da wannan tuhuma, shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki, ya kalubalanci Farfesa Jega akan bayyana sunayen 'yan majalisar masu hannu cikin wannan kazanta ta rashawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel