Daya daga cikin Sanatocin jihar Kaduna ya caccaki El-Rufa’i, ya kira shi takadari

Daya daga cikin Sanatocin jihar Kaduna ya caccaki El-Rufa’i, ya kira shi takadari

Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta Arewa, Suleiman Hunkuyi, ya caccaki gwamna El-Rufa’i, tare da kiran gwamnatin sa ta takadaranci.

Sanatan ya fadi hakan ne yayin da yake bayyana cewar gwamna El-Rufa’I na kokarin rushe masa gida duk da umarnin kotu ya hana shi yin hakan.

Daya daga cikin Sanatocin jihar Kaduna ya caccaki El-Rufa’i, ya kira shi takadari

Sanata Suleiman Hunkuyi

A wani rubutu da ya yi a shafin san a Facebook, Hunkuyi, ya ce, “gwamnatin jihar Kaduna zata rushe min gida na duk da umarnin kotu ya haramta mata yin hakan. Har a yanzu da nake wannan rubutu, maganar na gaban kotu, ba a yanke hukunci a kanta ba amma gwamnatin ta tubure a kan rushe min gida.”

DUBA WANNAN: Kachikwu ya ce zai ajiye mukamin sa na ministan man fetur

Sanatan ya kara da cewar, wannan ba shine karo na farko da gwamnatin jihar Kaduna ta ki yin biyayya ga umarnin kotu ba tare da bayyana cewar mutanen Kaduna na sane da wannan halayya ta kin mutun ta doka da gwamnatin jihar ke yi.

Hunkuyi ya bayyana mamakin sa bisa yadda gwamnatin jihar ke garzayawa kotu domin karar jama’a a kan laifin da bai taka-kara-ya-karya ba amma ita ba zata iya girmama umarnin kotu a kan ta ba tare da bayyana cewar ba zasu zuba ido su kalli gwamnatin na yiwa jama’a yadda take so ba, ba tare da an kalubalen ta ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel